Ashe
Shugaba Buhari ne ya nemi El-Rufa’i ya rubuto masa takarda
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya
rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki inda ya fada masa cewa akwai
gyara a tafiyar. Sai dai yanzu mun gano dalilin da ya Malam Nasir El-Rufa’i ya
rubuta wannan takarda
Kwanan nan aka samu labarin
cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wata wasika ga
shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake kiran sa da yayi maza yayi wasu gyara
a mulkin sa, ciki dai ana bukata ya sallami wasu na kusa da shi irin su Abba
Kyari da Babachir Lawal.
El-rufa'i lokacin da ya kai ziyara Daura wajen Buhari
Sai dai bincike da wata
Jarida tayi an gano cewa ashe shugaba Buhari ne da kan sa ya nemi Malam Nasir
El-Rufa’i ya rubuta wannan takarda a sa’ilin da su ka hadu a Garin Daura
lokacin bikin Sallah a Satumban bara.
Dama can an yi taro da
Kungiyar Arewar nan ta ACF inda suka nemi a fadawa Buhari cewa ya tsige
Sakataren Gwamnatin sa da kuma Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati. Haka kuma
Gwamna El-Rufa’i ya rubuta cikin takardar ta sa bayan nazari.
Rahotannin sun nuna cewa
wasu na kusa da shugaban kasar ne su ka fito da takardar Duniya ta gani domin a
dauka cewa Gwamna El-Rufa’i yana yi wa Shugaba Buhari zagon kasa ne. Wasu dai
na ganin cewa siyasar tana kadawa ta wajen Gwamnan na Jihar Kaduna kuma suke
kokari su taka masa birki.
No comments:
Post a Comment