Friday, March 3, 2017

MMM: ‘Yan Najeriya sun tafka katuwar asara




Kusan mutane miliyan 3 na Najeriya suka tafka muguwar asara bayan tsarin nan na MMM ya rushe Inji shugaban Hukumar NDIC

Shugaban Hukumar NDIC Umaru Ibrahim yake bayyana cewa ‘Yan Najeriya kimanin miliyan 3 ne ta sha da su misilla bayan tsarin cacar nan na MMM ya rushe. Umar Ibrahim yace ya samu wannan bayanan ne a kafafen yada bayanai na zamani.

Idan ta tabbata kamar yadda ya zo a Jaridar Daily Trust, Najeriya tayi asarar Naira biliyan 18 a tsarin nan na MMM mai nunka kudi. Shugaban NDIC din ya bayyana haka ne a jiya wajen wani taro da aka yi a kasuwar baja-kolin Duniya a Kaduna.

Tun dama can an gargadi ‘Yan Najeriya game da irin wadannan tsare-tsare, sai dai Jama’a da dama suka yi kunnen-kashi, to ga irin ta nan dai, yanzu makudan kudin Jama’a da dama ya tafi har abada.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...