Ana ta faman yada cewa tsohon
shugaban kasa Yakubu Gowon ya samu cikawa. Sai dai wannan labari ya rudar da
‘Yan Najeriya. Shin da gaske ne Gowon din ya cika ko kuwa?
Gidan
yada labarai na NTA na kasa ya sanar da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya
Yakubu Gowon ya samu cikawa gidan gaskiya. NTA ta ce shugaban ya bar Duniya ne
yana mai shekaru 79 da haihuwa yayin da ake haska labarai.
Sai
dai da alamu subuta ce aka yi don kuwa wata mata ce mai suna Martha Kande Audu
ta cika. Martha tayi aiki da gidan rediyo da talabijin na Jihar Kaduna wanda
asali ma ita ce macen farko da aka fara jin muryar ta a gidan rediyon.
Martha
Kande Audu ‘yar uwar tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ce kuma ta rasu tana da
shekaru 79 a Duniya. Wannan kuskure dai ya sa jama’a da dama cikin rudu. Yakubu
Gowon ya mulki kasar na shekaru kusan 9 a lokacin yakin basasa na Biyafara.
A
jiya ne kuma shugaba Muhammadu Buhari
ya taya tsohon shugaban kasa Obasanjo murnar cikan sa shekara 80 a Duniya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa Olusegun Obasanjo ta wayar tarho daga
Landan. Shugaba Buhari ya kira Obasanjo ya cigaba da kokarin kawo hadin-kai.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment