Man Utd ta tashi daga na 6 bayan
rabin shekara
Kungiyar
Man Utd ta tashi daga mataki na 6 wanda ta dade a kai a wannan makon. Yanzu
haka Man Utd ta dawo mataki na 5 inda ta kerewa Kungiyar Arsenal. Sai dai
abubuwa na iya cabewa idan Man City da sauran manya suka ci wasannin su.
Man
Utd dai tayi nasara ne bayan ta doke Kungiyar M/Boro da ci 3-1. Wannan ne kusan
wasa na farko bayan Kungiyar M/Boro ta kori Kocin ta wanda tsohon Mataimakin
Koci Jose Mourinho na Man Utd ne Aitor Karanka.
Marouane Fellaini da Dan wasa Smalling su ka
jefa kwallaye a raga. Shi ma dai Dan wasa Jese Lingard ya zura kwallo mai kyau.
Alvaro Negredo na Kungiyar Boro ne ya ci wa Kungiyar kwallo guda. Man Utd dai
ta kai kusan watanni 6 a mataki na 6 a gasar firimiya.
Kocin Man Utd Jose Mourinho
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment