Tuesday, March 14, 2017

JAMB ta kawo sabon tsari




Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare na ta kawo sabon tsari. Yanzu haka dai an rage wa’adin yin rajistar jarrabawar JAMB din.



Hukumar JAMB ta rage lokacin da ake dauka wajen yin rajista domin rubuta jarrabawar ta shiga Makarantun gaba da Sakandare a kasar. JAMB tace daga yanzu wata guda kurum za a bada domin yin rajista.

Shugaban Hukumar JAMB din Farfesa Ishaq Oloyede yace za a fara sayar da takardun jarrabawar ne a Ranar 20 ga wannan Watan, sannan kuma za a rufe saidawa a Ranar 19 ga Watan Afrilun gobe. Yanzu haka dai ana so har Makafi su fara zana jarrabawar.


Farfesa Oloyede ya bayyana haka ne a Legas yace wannan karo ba za a dauki dogon lokacin nan har na watanni uku ana rajista ba. Farfesan yace kuma ba za a kara wa’adin ba nan gaba don haka sai kowa ya garzaya yayi abin da ake bukata cikin lokaci.

Yanzu dai ana yin jarrabawar JAMB din ne da na’ura mai kwakwalwa. Za kuma a yi wani gwaji ga duk mai bukata domin shiryawa Jarrabawar da kyau Inji Hukumar, ko da yake dai ba tilas bane yin gwajin. 


 [NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...