Ronaldo yayi abin da ba a taba yi ba a kasar Spain
– Babban dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya bar tarihi a Duniya
– Duk kasar Spain babu dan wasan da ya kai Ronaldo zura
kwallaye ta kai
– Haka kuma Ronaldo ya fi kowa jefa
kwallaye a Filin Santiago Bernabeau
Zakaran
Duniya Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Duniya inda ya zama Dan wasan da ya
fi kowa zura kwallaye a raga da kai. A karshen wannan makon ne Ronaldo ya kara
jefa kwallo da kai a wasan su da Real Betis.
Yanzu
haka Ronaldo yana da kwallaye 46 da ya ci da kai tun zuwan sa kasar Spain. Duk
kasar dai ba a taba samun wanda ya ci irin wannan kwallaye a tarihi ba. Dan
wasa Aritz Aduriz ne dama can ya fi kowa inda ya ke da kwallaye 45.
Haka
kuma Ronaldo ne Dan wasan da ya fi kowa kwallaye a gida watau filin Santiago
Bernabeau. Cristiano Ronaldo ya buge tsohon Dan wasan Kungiyar Santillana mai
kwallaye 209 a filin wasan inda shi ya zarce haka.
Yanzu
haka dai Real Madrid tayi gaba a Gasar La-liga bayan ta doke Real Betis a Ranar
Lahadi. Sergio Ramos ne ya ci kwallon karshen a wasan.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment