Sankarau na cigaba da kashe mutane a Arewacin Najeriya
Cutar sankarau na cigaba da yaduwa a Jihohin
Arewa inda da dama su ke mutuwa a dalilin haka. Cutar yanzu ta uka Garin
Sokoto, Bauchi, Katsina da ma wasu Garuruwan.
Ma’aikatar
lafiya ta Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa cutar sankarau ta hallaka
mutum guda yayin da wasu kuma su ka kara kamuwa da cutar kamar yadda NAIJ.com
ke samun labarin a halin yanzu.
Dr.
Muhammad Kainuwa Darekta ne a ma’aikatar lafiya ya bayyana cewa cutar ta kashe
wani karamin yaro a Garin Gwaram. Haka kuma dai an samu yaduwa cutar a
Garuruwan Kiaywa, Gwaram, Maigatari da Kirikasamma.
Babbar
matsalar da ake fuskanta dai it ace rashin magunguna a Yankin, Dr. Kainuwa yake
cewa da zarar an samu magani za a ci karfin wannan mugun cuta wanda ta fara
addabar Yankin arewa musamman Sokoto, Bauchi da sauran su.
A Jihar
Sokoto Kwamishinan ya bayyana
cewa an samu aukuwar cututtuka fiye da sau 330 a Kananan Hukumomi 7. A ciki dai
an samu wasu da su ka bakunci lahira don yanzu haka dai annobar na ta kara
kamari inda ta ga bayan mutane akalla 21 a Garin.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment