Friday, March 10, 2017

Babban dan wasa zai ajiye kwallo


– Babban dan wasa Xabi Alonso zai yi ritaya


– Dan wasan na tsakiya ya yace daga kakar bana shikenan


– Alonso ya bugawa Liverpool da Real Madrid wasa




Babban dan wasan tsakiyar nan na kasar Spain Xabier Alonso Olano yace zai ajiye tamula a karshen wannan shekarar. Xabi Alonso ya bayyana wannan matakin da ya dauka ne kwanan nan, yace ba don yana so ba.

Alonso yace ya yanke wannan shawarar ne bayan yayi nazari. Xabi dai yana takawa kungiyar Bayern Munchen leda ne a yanzu haka. Xabi dan wasan tsakiya ne kwararre kuma mutum maras hayaniya a fili da waje.


Xabi Alonso ya fara kwallon sa ne a gida Real Socieded da ke kasar Spain, sannan ya wuce Liverpool inda ya ci kofin ‘Champions League’ daga nan ya komo Real Madrid inda ya kara samun nasarar lashe wannan kofi. Xabi zai ajiye wasa yana da shekara 35 yace tun kafin abin ya gagare sa.

A kasa kuma, Mai kula da ‘Yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya mikawa Ahmed Musa kambun Super Eagles a dalili da cewa kyaftin din kungiyar John Mikel Obi ba zai buga wasannin da za a kara masu zuwa nan gaba ba.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...