Wasu
Malamai daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Musulmai suyi riko da littafin
Al-Kur’ani mai girma domin su rabota a nan Duniya da lahira.
Wasu Malaman addini da
suka taso tun daga kasar Saudiyya sun yi kira ga Jama’a suyi riko da Littafin
Al-Kur’ani mai girma. Malaman suka ce riko da littafin Allah ne kadai zai kai
Jama’a ga shiriya Duniya da kuma Lahira.
Malaman dai sun taso ne
daga Jami’ar Ummul-Qura ta cikin Birnin Makkah da ke Kasar Saudiyya inda suka
zo Najeriya kuma Jihar Kaduna. Sun zabi wurare inda suka yi wa’azi a Jihar daga
ciki akwai masallacin ITN da ke Zangon-Shanu Zaria.
Dr. Ahmad Al-Furaih da
kuma Dr. Ahmad Al-Huraisi da ke Jami’ar Birnin Makkah suka ce dole a komawa
Littafin mai tsarki domin a samu cigaba
a nan da ma gaba. Daya daga cikin Malaman yace idan har makarantun Kur’ani suka
lalace to al’umma ta lalace koda yake dai mutanen Najeriya suna da kokarin
karatun Al-kur’ani.
Dr. Al-Huraisi yayi
kira da Jama’a su yi koyi da darussan da ke cikin Al-Kur’ani irin na kisosshin
Annabawa. Riko da littafin dai bai tsaya a karatu ba kurum, ya hada har da aiki
da shi Inji Malaman kamar yadda mutanen da su gabace mu suka yi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment