Thursday, March 2, 2017

Wani Dattijo yayi wa Sanatoci gardama



An dai ga abin ban mamaki a Majalisar Dattawa wannan mako yayin da wani Dattijo yayi kememe ya ki bin umarnin Sanatocin. Dattijon yace: 'Ba za a rera National anthem din ba...'




Kwanan nan ne fadar shugaban kasa ta tura sunan wani zuwa ga Majalisa a matsayin Jakadan Najeriya. Ko da wannan Dattijo ya shiga Majalisar an ga abin mamaki a yayin tantance sa.

Sylvanus Nsofor mai shekaru 82 a Duniya tsohon Alkali ne a babban kotun kasar da kuma kotun daukaka kara duk na Najeriya, Nsofor ya kuma koyar a wata Kwalejin shari’a da ke Birnin Landan watau a kasar Ingila.

An dai aika sunan sa a matsayin daya daga cikin Jakadun kasar zuwa ga Sanatoci domin su tantance sa. Ko da Dattijon ya hallara gaban masu tantancewar sai wani Sanatan Jihar Legas Gbenga Ashfa ya nemi tsohon ya karanta taken kasar. Nan fa wannan tsoho mai sama da shekaru 80 a Duniya yace ba zai rera taken ba, hakan kuma aka kyale sa.

An dai haifi tsohon Alkali Sylvanus Nsofor a Garin Oguta na Jihar Imo a watan Maris na shekarar 1935 watau shekaru sama da 20 kafin Najeriya ta samu ‘Yancin-kai. Za a tura Mista Nsofor aikin jakadanci zuwa wata kasa.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...