Buhari zai yi kakkaba a Gwamnati; Za a canza
wasu Ministoci Inji Sahara Reporters
-- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi babban
sauyi a Gwamnatin sa -- Za a canza wasu Ministoci da manyan Jami’an
Gwamnati -- Zazzagar za ta taba wasu manyan kusoshi
Kusan shekaru biyu kenan
da kafuwar wannan Gwamnati ta shugaba Muhammadu Buhari, mun samu labari cewa za
a yi wasu sauye-sauye a Gwamnatin kwanan nan ba da dadewa ba. Sai dai Majiyar
ba ta bayyana sunayen wadanda abin zai taba ba. Za dai a ga shakuwar aiki
kwarai tsakanin shugaban kasar da Mataimakin sa bayan nan.
Majiyar da tayi magana a
boye saboda yanayin kakkabar, tace cikin wadanda za a taba akwai manyan
kusoshin da ke kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sannan kuma dai Gwamnan
CBN Godwin Emifiele yana cikin wadanda za su iya bada wuri.
Za kuma dai a cike
guraben Ministocin Jihar Kogi da Gombe, wanda daya ya mutu yayin da daya kuma
ta bar aikin zuwa Majalisar dinkin Duniya. Za kuma dai a sauya guraben
Ministocin da ba su jituwa.
Ba mamaki kuma a rage wa
Ministan ayyuka da wuta da gidaje Babatunde Fashola aiki a sauyin da za a gani.
Cikin kusoshin da za su iya tafiya dai akwai Abba Kyari da kuma Babachir Lawal
watau shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati da Sakataren Gwamnati. Sai dai mai
magana da bakin shugaban kasar yace bai san maganar ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment