Matan Chibok: An bar hannun Boko Haram ba a
koma gida ba
A watan Afrilun 2014 aka sace ‘Yan mata sama
da 200 daga wata Makaranta da ke Garin Chibok a Jihar Borno. Ko ya rayuwar
wadannan mata ke kasancewa bayan sun bar hannun Abubakar Shekau?
Tun bayan da aka sace
wadannan ‘Yan mata dai aka fara kuwwar cewa a gano su, daga nan ne ‘Yan Boko
Haram suka fahimci cewa sun yi babban kamu; Hakan har ta sa aka fara karrama ‘Yan
matan Chibok dabam da sauran ‘Yan mata Inji wasu daga cikin ‘Yan matan da aka
kama har su ka auri ‘Yan ta’addan. Kai wata tace har bayi aka ce ta zaba cikin
sauran matan.
Da alamu dai Gwamnati
ta biya ‘Yan ta’addan wani abu kafin a saki wasu daga cikin ‘Yan matan.
Kungiyar nan ta Red Cross ta Duniya da Gwamnatin kasar Switzerland ne suka
shiga cikin yarjejeniya da ‘Yan Boko Haram. Bayan an saki yaran dai iyayen su
sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja.
Sai dai fa har yanzu
wadannan yara ba su dawo gida ba, don kuwa suna nan boye a wani wuri inda ake
kokarin kara jirkita tunanin su daga abin da suka ci karo da shi a baya hannun ‘Yan ta'addan Boko Haram.
Yanzu dai wata tace sau biyu kurum ake bari suyi waya da iyayen su
a mako inda aka saka su a wata Makaranta. Sai lokacin hutun Kirismeti ne kadai
dai aka bari yaran suka gana da iyayen su, wanda hakan ba ya masu dadi.
NAIJ.com Hausa suka
fassara wannan daga Jaridar NY Times ta Amurka
No comments:
Post a Comment