HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN
ITN-ZARIA
Ni’imar Musulunci-Daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar
A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim, BismilLahir Rahman
Ar-Raheem,
Dukkan Godiya sun tabbata ga Allah SWT Mai iko da daukaka,
Gwamnin Sarki mai hikima mai adalci sannan Masani a cikin al’amuran Sa. Muna
shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah SWT; Wannan shaidawa ce
wanda muke fata a dalilin ta mu samu tsira daga azaba mai radadi. Kuma muna
shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon ne
Wanda aka aiko da gaskiya.
Bayan haka:
Hakika Allah yayi mana ni’ima da wasu ni’imomi masu
dinbin yawa; idan da za mu lissafa su duk, to ba za mu iya ba. Daga ciki akwai
ni’imar ji, gani, hankali, lafiya, dukiya, ‘ya ‘ya, iyali; mace da namiji, da
kuma wasu masu dinbim yawa dabam. Sai dai duka wadannan ni’imomi suna karewa ne yayin da
rayuwa ta kare. Amma akwai ni’ima guda wanda ke dogewa har ga lahira; ita ce
mafi girmar ni’ima watau ni’imar musulunci. Don ita wannan ni’ima ita ke bambanta tsakanin
mai imani da rafkananne, tsakanin mai biyayya da mai sabo, tsakanin Musulmi da kuma kafiri. Saboda haka
tasirin wannan ni’ima na bayyana a nan Duniya da kuma lokacin mutuwa da kuma Lahira. Shi
musulunci shine Addinin da Allah ya zaba mana ya kuma yardawa bayin sa a
lokacin da Annabi SAW yake aikin hajjin sa na ban-kwana. Allah SWT yace: A yau na kammala maku addinin ku, na kuma cika maku ni’ima ta, na kuma yardarm
maku musulunci a matsayin addinin ku. Malamai suka ce ‘Ni’ima Ta’ a wannan
ayar ita ce musulunci.
Madalla da wannan baiwa da wannan ni’ima ta Allah da ya
kammala mana addini. A Duniya abin da ake nufi da musulunta shi ne a ce mutum na bin tafarkin
shari’ar Allah a rayuwa. Allah SWT ya halicce mu ya kuma saka mu kalifofin sa a
bayan kasa domin kawai mu aiwatar da tafarkin sa a doron kasa. Ko a Duniya sai
ka ji ance an aika wani a matsayin jakadan Najeriya a wuri kaza, duk wanda aka
aika jakada, abin da ake so a gare sa shi ne ya kare muradu ya kuma tafiyar da manufar
Najeriya a wannan kasar da aka aika sa. Saboda haka abin da Allah SWT yake so a
gare mu shi ne mu
tafiyar da rayuwar mu ga shari’ar sa a cikin kowane al’amari daga cikin al’amurran
rayuwar mu. Abin da ake so komai za muyi ya zama mun samu lada saboda mun yi
tamkar yadda Allah yace; duk abin da aka yi kamar yadda Allah yace aka kuma yi domin kuma yardar
sa to ya zama ibada. Allah
madaukaki yake cewa: ‘Ban hallici aljannu da mutane ba face don su bauta mani…’
Watau yadda Allah yace kuma domin neman yardar sa. Madalla dai da wannan ni’ima
da Allah ya zabe mu a matsayin al’umma ta tauhidi wadanda za su daukaka kalmar ‘La-ila-ha-illal-Lah.
A kan wannan ne dai aka riko aiko da Annabawa. Da ace za mu rika godiya ga
Allah muna masu sujuda har zuwa tashin kiyama, ba za mu iya abin da ya dace na
godiya ba.
Allah madaukakin Sarki ya fada a cikin Al-kur’ani ga
Manzon Sa cewa: ‘Wasu har suna goranta maka (watau Annabi SAW) cewa sun
musulunta tamkar sun yi maka wata alfarma….’ Ka (Kai Annabi SAW) fada masu
cewa: ‘ka da ku goranta mani musuluncin ku, ni ku ka yi wa alfarma ko ni nayi
maku alfarma?’ Bari Allah ne ya shiryar da ku zuwa ga imani. Wannan shi ne
gaskiyar lamari idan har kun tabbata masu imani’ Saboda haka dai ni’imonin
Allah SWT suna da yawa amma wannan ni’ima wanda Allah yayi mana baiwa da ita, ita ce babbar ni’ima. Allah
SWT
fa
ya riga ya fada cewa: Addini karbabbe a wajen Allah
shine Musulunci; don haka Allah ba zai karba daga wani ba addini dabam idan ba musulunci
ba, kana a Lahira zai zama cikin masu asara. Allah yayi mana ni’ima wanda a
dalilin ta ya fada mana cewa Ku (Musulmai)
kun kasance mafificiyar al’umma da Ubangiji ya fitar a doron kasa domin amfanin
mutane… kuma dai kullum za ku rika umarni ga alheri tare da hani daga mummuna…
Wannan dai shi ne ya mayar da ku dabam cikin sauran al’umma.
Sai dai kuma fa imani ba ya kasancewa ta hanyar buri ko
magana da baki ko takama da ado da sunan musulunci kadai. Malamai suka ce imani
shi ne abin da ya tabbata a cikin zuciya kana kuma aikin mutum ya gaskata haka.
Idan ya zamana kana takamar kai musulmi ne amma ka buge da ayyukan assha, to
ina musuluncin? Ka ga watau dole muyi bakin ciki a wannan lokaci saboda irin
yadda mutane Musulmai su ke aikata aiki na assha, cin amana da barna a wurare
da dama. Wannan abin takaici ne wanda ya shafi mutane tun daga saman su har kasa; watau ba
wadanda ke rike da manyan mukamai kurum suke da wannan hali ba, har wani da
kake ganin sa abin tausayi yana da irin wannan hali, yana kokari ya ci amanar wani
har ma ya iya kashe wani. Duk a haka dai muna cewa mu musulmai ne. Wane irin
musulunci ne wannan? Idan har mun yarda cewa mu musulmai ne wadanda Allah yayi
mana ni’ima, to mu rike musuluncin nan mana; a gidajen mu da sauran wuraren
mu, ya zama duk wanda muka yi mu’amala da shi zai ce mun fita dabam, mu kuma muna fada masa
cewa ai musulunci ne wannan! Don me ba zai kasance haka ba? Don me za a wayi
gari har Musulmi
yace gara ya ba
Kafiri amana don
musulmi bai da rike-amana.
Wannan musiba ce! Me zai hana mu tambaya idan har ba mu san wannan addini ba, har ya zama shi
muke yi tare da iyalan mu da makwabtan mu da sauran wuraren ayyukan mu?
Saboda haka ‘Dan
uwa musulmi mu godewa Allah da wannan ni’ima, mu sani fa ba kurum cewa nagode
bane. A’a
dole
mu yabi Allah muyi godiya sannan a ga muna da’a wanda shi ne babban godiya.
Hakika shi Manzon Allah SAW an umarce sa da cewa: ‘Lallai salla ta da duk yanka
ta da rayuwa ta da mutuwa ta… Zan yi su ne ga Allah Ubangiji babu wani abokin
tarayya a gare Sa…
da haka aka yi mani umarni kuma Ni ne farkon wanda ya mika wayau watau Musulmi’. Haka aka
umarci Manzo SAW wannan ya sa duk mai hankali ya kamata yayi koyi da wannan.
Ana so duk abin da musulmi yake aikatawa idan ka tambaye sa, ya fada maka cewa
wannan shari’ar musulunci ce; haka ake zama musulmi!
Allah ka ba mu fahimtar Addinin musulunci sannan ka tseratar da ni
da ku duka daga azaba
mai radadi ka
shigar da mu gida na ni’ima. Allah ya karbi ayyukan mu tare da dadin tsira ga
Annabin Mu da Iyalan Sa da wadanda suka yi imani da Shi zuwa Ranar karshe. Allah
ka tabbatar da yardar ka kalifofin Manzon Allah SAW hudu da sauran sahabai, Ka samu cikin Mabiyan
Su. Allah ka buwayar
da addinin
musulunci
ka rusa abokan gaban sa. Allah ka ba mu zama lafiya ka raya mana kasa cikin alheri ka tsrerar da
mu daga duk wata fitina. Allah ka jagoranci shugabannin mu zuwa abin da kake so
ka
kuma
yarda da shi. Allah ka ba mu ka kara mana lafiya ka jikan wadanda suka rasu. Allah
ka ba shugaban kasar mu lafiya ka dawo mana da shi lafiya.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment