– Shugaban kasar Ghana ya kafa tarihi a kasar sa
–
Sabon shugaban ya nada Ministoci 110
– Jama’a
dai na ta kuka game da wannan lamarin
Sabon shugaban kasar Ghana
Nana Akufo-Addo ya nada Ministoci sama da 100 a Gwamnatin sa. Shugaban dai yayi
alkawari zai rage kashe kudin da Gwamnati take yi sai kuma ga shi ya kara yawan
Ministocin kasar wanda yace ya zama dole ne domin ayi gyara.
Shugaba Nana ya nada
mataimakan Ministoci har 50 tare da Ministocin Jihohi guda 4 bayan kuma dai ga
asalin manyan Ministoci har guda 56. Hakan dai na nufin Ghana na da Ministoci
har 110 kenan a yanzu wanda ba a taba yin hakan ba a tarihi.
Jam’iyyar adawa dai ta soki
wannan tsari inda kowane Minista yake da motoci da man fetur kyauta da kuma
gida da masu gadi ga makudan albashi na akalla $4000 a kowane wata. Wasu
Ma’aikatar dai akwai Ministoci har 5.
A Najeriya kuma Tsohon shugaban
kasa Dr. Jonathan Goodluck yayi kira ga ‘yan siyasar kasar da su zama masu
gaskiya a duk inda su ke. Jonathan yace masu rike da makamai su yi abin da ya
dace na taimakon talakawa a lokacin da suke kan mulki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment