Thursday, March 2, 2017

Tattalin arzikin Najeriya ya fara farfadowa



– Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki


Sai dai an kusa fita daga cikin wannan radadi Inji fadar shugaban kasa


– Alkaluma sun nuna cewa Najeriya na farfadowa





Fadar shugaban kasa tace Najeriya ta kama hanyar fita daga radadin tattalin arzikin da ake ciki. Najeriya dai na fama da durkushewar tattalin arziki tun bara bayan farashin mai ya rushe.

Alkaluman bincike su nuna cewa Najeriya na yin gaba idan aka yi la’akari da jimilar kudin kasar na GDP na karshen wancan shekarar. Mai ba shugaban kasa shawara game da harkokin tattalin arziki Dr. Adeyemi Dipeolu ya bayyana haka Inji mai magana da bakin mukaddashin shugaban kasa.

Najeriya dai ta samu ci-bayan tattalin arziki ko da dai bai kai yadda aka sa rai na tabarbarewar ba. Dr. Dipeolu yace alkaluman sun nuna cewa kasar na kokarin fita daga cikin halin durkushewar arzikin da ta ke ciki.

Kamfanin man Najeriya na NNPC ya bayyana cewa man da kasar nan ke hakowa a kowace rana ya kara yawa. Ana samun gangar mai sama da miliyan 2. Da alamu dai rikicin yankin na Neja-Delta yayi kasa. Shugaban Kungiyar OPEC Sanusi Barkindo yace yayi mamakin yadda Najeriya ta tsira daga kangin da aka shiga na tattalin arziki bayan da mai yayi kasa.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...