Monday, March 6, 2017

Shugaba Buhari ya kira gida Najeriya






Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a wayar tarho daga Landan. Ga dai yadda ta wakana tsakanin shugaban kasar da Gwamna Bello. 

Mun samu labari cewa shugaba Buhari wanda ke Birnin Landan inda yake hutawa yayi waya da Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello. Majiyar tace shugaba Buhari ya matsu ya dawo Najeriya domin ya cigaba da aiki.

Shugaban kasar ya kira Gwamnan Jihar Kogi ne lokacin yana tare da kakakin Majalisa da kuma wasu Kwamishinonin sa. Shugaba Buhari ya gode da kokarin Jama’a da ke tayi masa addu’a a ko yaushe.


Haka kuma Muhammadu Buhari ya kira tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a wayar tarho daga Landan domin taya sa murnar zagayowar ranar haihuwar sa. Obasanjo ya cika shekaru 80 da haihuwa a jiya.

Idan muka koma wani bangaren kuma, dubban mutane ne suka fito suka yi wa shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari addu’a ubangiji ya maido sa lafiya a Birnin Zazzau. Yanzu haka dai shugaba Buhari ya share fiye da wata guda da rabi a Landan.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...