– Mai
kudin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya fi shugaban kasar Amurka kudi
–
Arzikin Dangote ya fi jimilar abin da Trump da Oprah suka mallaka
– Mujallar
Forbes ta Duniya ta bayyana haka
Jaridar Forbes ta bayyana
cewa arzikin mai kudin Najeriya da ma Afrika Alhaji Aliko Dangote ya fi abin da
shugaban kasar Amurka Donald Trump ya mallaka. Trump dai kasurgumin attajiri ne
tun tuni amma Dangote ya sha gaban sa nesa ba kusa ba.
Bari ma dai dukiyar Dangote
ta fi ta Donald J Trump hada da na bakar ‘yar kasuwar nan Oprah Winfrey ta
Amurka. Dukiyar Dangote a yanzu haka ta kai akalla Dala biliyan $11 wanda ya
ribanya abin da Trump mai Dala biliyan 3.7 da Oprah mai Dala biliyan 3 suka
mallaka.
Dangote dai ya taba shigowa
cikin sahun mutane 25 da suka fi kowa arziki a Duniya shekaru 3 da suka wuce.
Shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf
Nahiyar Afrika.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment