– Yawan
man da Najeriya ke samu ya kara yawa
–
Da alamu an rage samun fasa bututun mai daga yankin
Neja-Delta
– A
cikin ‘yan kwanakin nan dai har Naira ta tashi
Kamfanin man Najeriya
na NNPC ya bayyana cewa man da kasar nan ke hakowa a kowace rana ya kara yawa.
NNPC tace a kullum
Najeriya na samun gangar mai sama da miliyan 2. Ko da yake dai ba bayyana
dalilin karin ba.
Shugaban Kamfanin na NNPC Maikanti Baru ya bayyana
haka yayin da ya zanta da ‘Yan jarida a Abuja. Mista Baru yace ana sa ran zuwa
karshen shekara a rika samun sama da ganga miliyan 2.2 a kowace rana.
Da alamu dai rikicin yankin na Neja-Delta yayi kasa
don kuwa kwana biyu ba a fasa wani bututun mai ba. Mukaddashin shugaban kasa
Farfesa Osinbajo dai yayi ta ziyarar yankin kwanki domin kawo karshen rikicin.
Shugaban OPEC M. Sanusi Barkindo yace yayi mamakin yadda Najeriya
ta tsira daga kangin da aka shiga na tattalin arziki bayan da mai yayi kasa.
Barkindo yace yanzu haka an yi mai wuyar don kuwa farashin mai ya daga a
duniya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment