Madalla: Dala na kara yin
kasa
Kamar dai yadda ku ka samu
labari a jiya ne farashin dalar Amurka ya kara saukowa kasa zuwa N360 wannan
dai ba karamin abin murna bane.
Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun
kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna.
A jiya ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika sayarda
dala a kan N360 daga kusan N370 da yake.
CBN ke cewa dole bankuna su dabbaga wannan doka domin
a ko yaushe ana iya zuwa bincike. CBN din dai ya gargadi bankuna da su guji
sayar da dalar da kowa face wanda yake neman kudi zai fita kasar waje karatu ko
asibiti.
Yanzu dai dalar tayi araha da sauki a gari domin kuwa
a cikin kwana guda ko biyu rak mutum zai samu kudin da yake so domin fita kasar
waje. An dai haramtawa bankuna sayar da dala ga ‘yan canji a waje.
Yanzu haka dai CBN ta saki makudan miliyoyin dala
wanda hakan ya sa ‘yan canji su ka sha kasa. A wancan makon kadai ‘yan canji
sun rasa sama da Naira Miliyan 100. Dama dai NAIJ.com ta rahoto cewa ‘Yan
kasuwa masu canjin kudi sun fara kokawa da lamarin tun tuni.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment