Thursday, March 2, 2017

Najeriya za ta daina shigo da man fetur?


– Ministan fetur na kasa Dr. Ibe Kachikwu yace ya zama dole Najeriya ta daina shigo da man fetur


Ibe Kachikwu yace nan da shekarar badi NNPC za ta rika tace duk man da Najeriya ke bukata


– Ministan fetur din yace abin kunya ne a ce sai Najeriya ta shigo da tacaccan mai





Karamin Ministan man fetur na kasa Dr. Ibe Kachikwu yace ya zama dole Najeriya ta daina shigo da man fetur ba da jimawa ba. Kachikwu ya bayyana haka ne a wajen wani taron da ake yi na harkar man fetur a Garin Abuja.

Ibe Kachikwu yace zuwa shekara mai zuwa da kuma ta gaban ta, ya kamata Najeriya ta fara tace duk kayan man da ta ke bukata ba tare da an shigo da shi daga kasar waje ba. Ministan yace abin kunya ne a ce Najeriya na shigo da tacaccen fetur bayan muna danyan fetur a kasa.

Ministan yace Kamfanin NNPC za ta rika tace duk man da Najeriya ke bukata maimakon a shigo da shi daga waje. Dr. Ibe Kachikwu yace ya kamata a tada matatun kasar wanda ba su aiki yadda ya dace.

Kwanaki Shugaban Kamfanin NNPC Maikanti Baru ya bayyana cewa man da kasar nan ke hakowa a kowace rana ya kara yawa. NNPC tace a kullum Najeriya na samun gangar mai sama da miliyan 2. Ko da yake dai ba bayyana dalilin karin ba.



[NAIJ Hausa]








No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...