Kwanakin
baya ne Majalisar Dinkin Duniya ta dauke Ministar Buhari, yanzu haka har an
rantsar da ita a matsayin mataimakiyar shugaban majalisar a Birnin New York da
ke Amurka.
Majalisar Dinkin Duniya
watau UN ta rantsar da ‘Yar Najeriyar nan kuma tsohuwar Ministar kasar Amina J. Mohammed jiya a matsayin mataimakiyar
shugaban majalisar a ofishin Majalisar da ke Birnin New York na kasar Amurka.
Antonio Gutierrez wanda
ya zama Shugaban Majalisar na 9 a Tarihi, ya nada Amina J. Mohammed a matsayin
Mataimakiyar sa tun watan Disamba sai dai ba ta fara aiki ba sai kawo yanzu
saboda tana rike da ofishin Minista a Najeriya inda ta ke kokarin kammala wasu
ayyuka.
Amina ce dai ‘Yar
Afrika ta biyu a tarihi da ta taba rike wannan matasayi a Majalisar dinkin
Duniya. Amina Muhammad ta zama wata abin koyi ga matasa masu tasowa. Tun ba yau
ba dai ta fara aiki da Majalisar dinkin Duniyar watau UN ta kuma taka
rawar-gani.
[NAIJ Hausa]
Allah Ya taya ta riko Ya kuma Yi Mata jagoranci Na alkhairi. Allah ka ba Amina J Muhammad Yi addinin ka hidima da wannan matsayi a UN.
ReplyDeleteAmeen
ReplyDelete