Saturday, April 1, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA


HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA



Godiya ga ni’imar Allah daga Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar


A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim, BismilLahir Rahman Ar-Raheem,

Dukkan Godiya sun tabbata ga Allah SWT, shi ne mai karamci da baiwa ga bayin Sa. Muna godiya da yabo gare sa Madaukakin Sarki. Shi ne mai yin falala dabam-dabam ga bayin sa da kuma nau’o’i dabam-dabam na ni’ima. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face Allah SWT, Shi kadai yake, babu abokin tarayya a gare Sa. Muna shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne.

Bayan haka:
Ya ku ‘Yan uwa mu ji tsoron Allah Madaukakin Sarki kuma mu gode maSa bisa ni’imomin da yayi mana, mu kuma sani cewa Allah ne kadai mai ni’ima kuma gare Sa muke fatar ayi mana ni’ima a Duniya da kuma lahira. Allah SWT yana cewa: Idan ku kace za ku kidaya ni’imomi na, ba za ku iya lissafe su ba. Lallai Allah mai yawan gafara ne mai kuma yawan jin-kai.

Saboda haka Bayin Allah ku gode masa bisa ni’imomin da yayi maku domin kuwa godiya na daga cikin dalilan su ke sa Allah ya kara kuma ya wanzar da ni’ima. Don saboda kafircewa ni’imar Allah kuma sai ya zama ni’imar nan ta tawaya ko kuma ta gushe gaba daya. Allah SWT yana cewa a Kur’ani: Idan ku ka gode, lallai Ni zan kara maku...Lallai kuma idan har ku ka kafirce, azaba ta tana da tsanani. Allah Mai tsarki yana dada fada a cikin Kur’ani inda ya bada misali da wata Al-karya Yake cewa tana cikin aminci da kwanciyar hankali da arziki, amma sai su ka kafirce daga ni’imomin Allah, sai kuwa aka dandana masu tufafin yunwa da tsoro saboda abin da suka kasance suna aikatawa na kafirci.

Ya ku ‘yan uwa ya ake godewa Allah da ni’imomin sa? Wannan yana cikin dagewa wajen bin umarnin Ubangiji Ta’ala muddin aka ce Allah yayi umarni a aikata kaza ko a bari sai mutum yayi iyawar sa ya aikata ko ya bari in dai har wannan umarni ya zo daga Littafin Allah ko bakin Annabin Sa SAW. Lallai fa mai sabon Allah ba mai godiya bane ga Ubangiji ko da ya ta furta cewa ‘Na godewa Allah.’ Ina amfanin mutumin da ke fada da harshe cewa yana godiya alhali yana ta sabawa Allah? Ko shin wannan mutumi ba ya tsoro a ce da shi karya ka ke yi. Allah SWT da ya tashi sai ya hallice ka mutum kuma mai hankali, sannan kuma ya ba ka musulunci da sauran ni’imomi, don haka Ubangiji ya cancanci godiya. Mu sani dai cewa mafi girman ni’ima kenan shiriya zuwa ga Musulunci. A yayin da ku ke Musulmai masu imani wasu na can suna dimuwa; wasu na cikin fushin Ubangiji na take sani, wasu kuma na cikin duhun Jahilci ba su ma gane wanene Ubangiji ba. Saboda haka duk wanda Allah ya azurta da Musulunci ya samu abu biyu; sanin gaskiya da kuma biyayya gare ta. Wannan ya bambanta mutum da Yahudu da su ka take sani da kuma Nasara da ba su san gaskiya ba su ke cikin duhun jahilci.

Manzon Allah SAW ya nuna mana yadda ake godiya ga Allah SWT ban da irin Salloli da yake yi, duk wani karamin abu sai Manzo SAW ya godewa Allah. Sai mu tambayi kan mu kamar yadda Annabi SAW yake tsayawa Sallar Nafila cikin dare, shin kai raka’a nawa kayi jiya cikin dare domin nuna godiyar ka ga Allah? Manzon Allah ya kan yi addu’ar godiya ga Allah da ya raya sa kuma bayan ya tashi daga barci. Kai ko jiya da ka farka ka fadi haka? Ko ba ka san cewa ni’ima ba ce da Ubangiji Ta’ala ya farkar da kai bayan ka kwanta. Ko da ka shiga ban-daki ka yi uzuri ka fito cikin sauki kayi irin abin da Annabi SAW yake yi? Annabi SAW yana addu’ar godiya ga Allah da ya samu damar kawar da abin da ke cikin jikin sa. Sannan Manzon Allah SAW ya kasance idan ya ci abinci (duk da Annabi SAW ba ya cin wani abinci sosai) yana godiya ga Allah iri dabam-dabam. Kai yau bayan ka karya kumallo da safe mai ka fada na godiya, watakila har da gyatsa kayi. Ko ba ka dauka cewa kokon da kosai da ka samu ni’ima bane? Wani bai samu ko kokon da ka samu ba domin ya sha, wani kuma ga kokon amma bai isa ya sha ba saboda wani hali na rahin lafiya ko aminci. Haka kuma Manzon Allah SAW yake yi idan zai kwanta barci cikin yini, watau dai kullum Manzon Allah cikin godiya yake. Shin mu haka muke? Ya kamata muyi koyi da Manzon mu Annabi SAW. Mu sani cewa duk wata ni’ima daga gare sa ta ke; babu mai badawa ko hanawa face shi. Idan har ka rasa wata ni’ima ta Duniya ka da ka zargi kowa kana cewa ‘Wane ya hani ni’, Allah Madaukaki ne bai ga dama ba. Haka kuma idan Allah Madaukaki ya ba ka kar ka butulce masa kana ‘Wane ya bani’, ba kowa bane shi face dan-aike. Allah SAW yana cewa a Kurani cewa: Duk abin da ku ka gani na ni’ima daga Allah ne, don kar ka dauka wani ya isa ko dabarar mu ce!

Allah ka ba mu fahimtar Addini ya sa ya amfane mu gaba daya. Allah ya karba mana ya tseratar da mu daga azabar wuta mai radadi, ya shigar da mu cikin gidan ni’ima. Allah yayi dadin tsira ga Annabin mu Muhammad SAW da Iyalan Sa da Sahaban Sa musamman Khalifofin Sa shiryayyu.

Allah ka taimaki Musulunci da Musulmai ka kuma kaskantar da Kafirci da Kafirai. Allah ka kare mu daga wata fitina da damuwa. Allah ka kara mana ni’imar ka da samun yardar ka. Allah ka tara mu a kiyama tare da Annabawan ka da kuma zababbun bayin ka.

Allah ka taimaki kasar mu ka taimaki shugabannin mu; ka kama hannayen su ka wanzar da al’amurar su. Allah ka shiryar mana da su ga abin da kake so kuma ka yarda da shi.


Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...