Ana kokarin ganin an hana Almajiranci a Arewa
Muhammad Malumfashi ya halarci taron
Wata
kungiya mai suna YouthHubAfrica na kokarin ganin yadda za a kawo karshen cin
zarafin kananan yara da ake yi a kasar nan musamman a Arewacin Najeriya. Don
haka ne ma dai aka shirya wani taro na karawa juna sani na kwanaki 3 a Garin
Kaduna wanda NAIJ.com ta samu halarta.
‘Yan
Jarida da sauran ma’aikata masu ruwa da tsaki daga Jihohin Kaduna, Kano,
Sokoto, Kebbi har ma da Jihar Oyo su ka halarci taron. Ana dai kokarin ganin
yadda Majalisun Jihohi za su kafa wannan dokar nan da ta kare hakkin kananan
yarada kuma dabbaka ta.
Bukky Shonibare a wajen taron
Dokar
za ta ba ‘ya ‘ya ‘yancin su auri wanda su ke so idan har sun girma sannan kuma
a ba su ilmi mai inganci tare da haramta masu talla da yawan bara wanda hakan
ke haifar da ‘da mara ido a al’umma.
An
dai gayyaci manyan mutane inda suka gabatar da lacca da kasida game da batun. A
mafi yawan Jihohin Arewa dai ba a kafa wannan doka da za ta ba yara ‘yancin su
ba. Wanda ba shakka wannan na cikin abubuwan da ke maido mu baya kamar yadda
Mawaki ya fada.
Taron karawa juna sani da YouthHubAfrica su ka gudanar a Kaduna
[NAIJ Hausa]
Allah Ya Ida nufi
ReplyDelete