Friday, March 31, 2017

Cutar sankarau ta shigo Jihohin Arewa


 Sankarau na cigaba da kashe mutane a Arewacin Najeriya




Cutar sankarau na cigaba da yaduwa a Jihohin Arewa inda da dama su ke mutuwa a dalilin haka. Cutar yanzu ta uka Garin Sokoto, Bauchi, Katsina da ma wasu Garuruwan.

Ma’aikatar lafiya ta Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa cutar sankarau ta hallaka mutum guda yayin da wasu kuma su ka kara kamuwa da cutar kamar yadda NAIJ.com ke samun labarin a halin yanzu.

Dr. Muhammad Kainuwa Darekta ne a ma’aikatar lafiya ya bayyana cewa cutar ta kashe wani karamin yaro a Garin Gwaram. Haka kuma dai an samu yaduwa cutar a Garuruwan Kiaywa, Gwaram, Maigatari da Kirikasamma.

Babbar matsalar da ake fuskanta dai it ace rashin magunguna a Yankin, Dr. Kainuwa yake cewa da zarar an samu magani za a ci karfin wannan mugun cuta wanda ta fara addabar Yankin arewa musamman Sokoto, Bauchi da sauran su.

A Jihar Sokoto Kwamishinan ya bayyana cewa an samu aukuwar cututtuka fiye da sau 330 a Kananan Hukumomi 7. A ciki dai an samu wasu da su ka bakunci lahira don yanzu haka dai annobar na ta kara kamari inda ta ga bayan mutane akalla 21 a Garin.



[NAIJ Hausa]

Za ayi amfani da 'Card reader' a zaben 2019


Majalisa ta kawo gagarumin sauyi a harkar zabe 


A zaman Majalisa Sanatoci sun amince ayi amfani da na’urar tantace masu zabe watau ‘Card Reader’ a zabe mai zuwa wanda wannan babban cigaba ne aka samu

A jiya ne Majalisar Dattawa ta amince da ayi amfani da na’urar tantace masu zabe wanda aka sani da turanci a matsayin Smart Card Reader. Majalisar tayi wa tsarin zaben kasar na 2010 garambawul domin gyara harkar zabe.



Shugaban Majalisar Bukola Saraki ya jagoranci zaman inda ya kuma tabbatar da wannan kudiri. Sanatocin kasar dai sun yi garambawul ne ga sashen na 52 na dokar tsarin zabe na kasar inda ta ba Hukamar INEC damar amfani da na’urori na zamani wajen gudanar da zaben.

Majalisar ta dai kawo garambawul da dama a harkar zabe daga cikin an tsaida kudin fom din takarar shugaban kasa da sauran masu takara. Majalisar ta kuma ragewa Gwamnoni karfi wajen zaben masu fitar da gwani a zaben farko.



[NAIJ Hausa]

Tattalin arziki: IMF ta jinjinawa Najeriya

IMF ta Duniya ta jinjinawa Gwamnatin Najeriya




IMF ta Duniya ta jinjinawa Najeriya wajen kokarin da tayi wajen fara shawo kan tattalin arzikin kasar wanda ya ruguje a shekaran bara

IMF mai bada lamuni ga kasashen Duniya ta yabawa Najeriya wajen irin kokarin da tayi na shawo kan matsalar tattalin arziki musamman wajen daidaita darajar kudin kasar na Naira wanda ya rugurguje.

Bankin kasar na CBN ya saki sama da Dala Biliyan guda ga bankuna domin farashin dalar yayi sauki a kasar. Wannan tsari da CBN ta kawo dai yayi aiki bayan a da ana tunani cewa Dalar na iya zarce N1000.

IMF din ta jinjinawa tsarin tattalin arzikin kasar inda ta ke fatan nan gaba ma abubuwa su kara kyau. IMF dai na neman ganin yadda za ayi masu jari su shigo kasar su ba-ja-kolin su. IMF din mai bada lamuni tace Najeriya na kan hanyar da ta dace.


[NAIJ Hausa]

Thursday, March 30, 2017

Tattalin arziki: Naira tayi sululu


Ka san nawa ne farashin Dala a Yau?





Bayan dogon lokaci dai darajar Naira na ta kara sama tun daga sama da N500 har zuwa N360 NAIJ.com na samun labari cewa yanzu kuma farashin dalar ya dan kara tashi

Farashin dala ya kara tashi bayan an dauki dogon lokaci dalar na yin kasa. An dai dauki kusan wata guda darajar dalar in ban da kasa kurum ba abin da yake yi. Da sai da darajar Dalar ya haura N500.

Sai dai daga jiya zuwa yau Naira ce ta sha kasa a kasuwar Duniya inda ta yi kasa a kan Dala daga kan N382 zuwa N385. Dalar Pounds ta Ingila kuwa dai ta kai N400 yanzu a kasuwar ‘yan canji kamar yadda NAIJ.com ke samun labari.

Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna kwanakin baya kamar yadda muka rahoto. A wannan makon ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika sayarda dala a kan N360.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar nan dai na murmurewa bayan ya ruguje a baya. Da alamu dai abubuwa sun dan fara mikewa a Najeriya.


[NAIJ Hausa]

Miliyoyin Jama’a na fama da karancin ruwan sha

Boko Haram: Miliyoyin Jama’a na fama da rashin ruwan sha


A dalilin rikicin Boko Haram Miliyoyin Jama’a na fama da rashin ruwan da za su sha a Yankin Arewa maso gabas kamar yadda NAIJ.com ta samu labari




A wani nazari da aka yi an gano cewa kusan mutane miliyan 4 ke fama cikin rashin ruwa a yankin da Boko Haram su ka yi ta’adi. Boko Haram dai sun barnata kashi 75% na hanyoyin ruwa a Yankin na Arewa maso gabas.

Rikicin Boko Haram dai ya bar dinbin miliyoyin Jama’a babu ruwan sha Inji Kungiyar UNICEF. Kungiyar mai kula da kananan yara tace a Jihar Borno ‘Yan Boko Haram sun gama bata duk wasu hanyoyin samun ruwan sha a Garin.

Karancin ruwan sha da kazanta da rashin lafiya na nema ya zama wani karin tashin hankali a Yankin kasar kamar dai yadda yake faruwa a kasashen Somaliya, Yemen da kuma Kudancin Sudan Inji UNICEF.

Karancin ruwan sha mai tsabta dai na haifar da cututtuka da dama musamman ga yaro karami. Boko Haram dai ba karamar barna su ka yi musamman a Yankin ba inda aka kashe miliyoyi yayin da wasu kuma su ka tsere.

Kwamishinan lafiya na Jihar Sokoto Dr. Balarabe Kakale ya bayyana cewa cutar sankarau kuma na cigaba da kashe mutane a Jihar Sokoto. Yanzu haka dai annobar na ta kara kamari inda ta ga bayan mutane 21.



[NAIJ Hausa]

Wednesday, March 29, 2017

FIFA ta dakatar da Lionel Messi

FIFA ta dakatar da Lionel Messi




FIFA ta Duniya ta dakatar da babban dan wasan nan na kasar Argentina Lionel Messi. Dan wasan gaban ba zai buga wasanni 4 ba bayan an same sa da laifin fadawa Alkalin wasa maganganun da ba su dace ba.

A Ranar Alhamis din da ta gabata ne Lionel Messi ya zagi daya daga cikin Alkalan wasa a wata fafatawa da kasar sa ta Argentina tayi da kasar Chile. Argentina ce dai tayi nasara a wasan inda kuma Messi din ne ya jefa kwallo guda a raga.


Dan wasan na Barcelona ba zai buga wasannin da kasar sa za ta kara domin zuwa gasar cin kofin Duniya ba. Argentina na shirin kece raini da kasar Bolivia yanzu haka. Sai dai kasar Argentina tace za ta daukaka kara.



Messi yayi wa Alkalin wasa rashin kunya


[NAIJ Hausa]

Wani Fursuna yayi Digir-gir daga gidan yari

Wani Fursuna yayi Digir-gir daga gidan yari; yana shirin komawa yayi Digir-digir



Farfesa Abdallah Uba Adamu

Fursunoni ma suna karatu a Najeriya kamar yadda shugaban Jami’ar NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana Ranar Litinin dinnan

Shugaban Jami’ar NOUN wanda ake karatu daga gida ya bayyana cewa wannan karo har da wani Fursuna ke shirin shiga karatun domin yayi Digirin sa na uku. Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana wannan a Abuja a wajen taron shugabannin Jami’o’i.



Gidan yari a Najeriya


Shugaban Jami’ar ta NOUN Farfesa Uba ya bayyana cewa Jami’ar su ce kadai ta ke da cibiya har a gidan yari. Farfesan ke cewa duk wani dan kason da ke sha’awar karatu sai yayi rajista kurum ya fara daukar darasi.

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana cewa yanzu haka akwai wanda ya kammala digirin san a biyu watau Masters yana kuma shirin fara na uku kenan watau PhD kuma duk a cikin gidan yari a daure. NOUN dai tana dauke da dalibai sama da 200, 0000 daga fadin kasar.


Jami'ar NOUN ta Najeriya



[NAIJ Hausa]

Tuesday, March 28, 2017

Dala: ‘Yan canji sun sha kashi


Madalla: Dala na kara yin kasa





Kamar dai yadda ku ka samu labari a jiya ne farashin dalar Amurka ya kara saukowa kasa zuwa N360 wannan dai ba karamin abin murna bane.

Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna.  A jiya ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika sayarda dala a kan N360 daga kusan N370 da yake.

CBN ke cewa dole bankuna su dabbaga wannan doka domin a ko yaushe ana iya zuwa bincike. CBN din dai ya gargadi bankuna da su guji sayar da dalar da kowa face wanda yake neman kudi zai fita kasar waje karatu ko asibiti.

Yanzu dai dalar tayi araha da sauki a gari domin kuwa a cikin kwana guda ko biyu rak mutum zai samu kudin da yake so domin fita kasar waje. An dai haramtawa bankuna sayar da dala ga ‘yan canji a waje.

Yanzu haka dai CBN ta saki makudan miliyoyin dala wanda hakan ya sa ‘yan canji su ka sha kasa. A wancan makon kadai ‘yan canji sun rasa sama da Naira Miliyan 100. Dama dai NAIJ.com ta rahoto cewa ‘Yan kasuwa masu canjin kudi sun fara kokawa da lamarin tun tuni.





[NAIJ Hausa]

Monday, March 27, 2017

Wani Lauya ya maka Israila kara a Kotu saboda kashe ‘Jesus’



- Wani Lauya a kasar Kenya ya maka mutanen kasar Israila kara a Kotu


- Lauyan yace mutanen Isra’ila ne su ka kashe Yesu Almasihu


- Wannan abu dai ya ba mutane mamaki





Wani Lauya mai suna Dola Indidis a kasar Kenya ya maka kasar Isra’ila a babban Kotun Duniya da ke Birnin Hague kara inda yake zargin mutanen kasar da kashe Yesu Almasihu wanda Musulmai su ke kira Annabi Isa kuma Kiristoci su ke bauta masa.

Lauyan yace kashe Annabi Isa da aka yi a bisa kan sarka ba daidai bane, zallar zalunci ne wanda ya saba hakkin bil adama. Babban Lauyan ya nemi a hukunta kasar Israila da kuma Sarkin Daular Rumawa a wannan lokaci da ma kasar Italiya.

Sarakunan Daular Rumawa ne dai su ka yanke hukuncin kashe Yesu wanda ake kira Jesus a wancan lokaci. Wannan babban Lauya na kasar Kenya yace dole a sake binciken shari’ar da aka yi don kuwa ba a bi ka’idar kotu ba.





[NAIJ Hausa]

Sunday, March 26, 2017

Allahu Akbar: Sai yanzu masana su ka gano amfanin dabino

Kimiyya ta gano abin da musulunci ya gano shekaru 1400 da su ka wuce



Tun fiye da shekaru 1400 da suka wuce a baya Addinin musulunci ya gano amfanin sukari a jikin jinjiri da aka haifa. Sai ga shi yanzu Kimiyya ta san da wannan nazarin. 

Wani ikon Allah, sai bayan shekaru sama da 1400 masana Kimiyya su ka fahimci cewa ashe jinjiri da aka haifa yana bukatar sukari nan take bayan haihuwar sa. Musulmai dai sun dade da sanin wannan tun ba yau ba.

Yana daga cikin Sunnonin Manzon Allah Annabi Muhammad SAW da ya koyar a dauki dabino dan kadan a tauna a sa wa jinjiri a baki da zarar an haife sa. Wannan abu dai shi ake kira Tahniqi da larabci.



A wani rahoto da Jaridar BBC tayi ya kuma samu zuwa hannun NAIJ.com, Masana kimiyya sun gano cewa yaron da aka haifa yana bukatar sukari kadan da zai hana kwakwalwar sa samun matsala.

A musulunci dai dabino ya zama wani babban abin marmari, wanda da shi ake so mutum ya fara buda baki a lokacin da yayi azumi domin kuwa yana dauke da sinadarai masu kara karfi da kuma matukar amfani.



[NAIJ Hausa] 

Ana kokarin ganin an hana bara a Arewa


Ana kokarin ganin an hana Almajiranci a Arewa



Muhammad Malumfashi ya halarci taron

Wata kungiya mai suna YouthHubAfrica na kokarin ganin yadda za a kawo karshen cin zarafin kananan yara da ake yi a kasar nan musamman a Arewacin Najeriya. Don haka ne ma dai aka shirya wani taro na karawa juna sani na kwanaki 3 a Garin Kaduna wanda NAIJ.com ta samu halarta.

‘Yan Jarida da sauran ma’aikata masu ruwa da tsaki daga Jihohin Kaduna, Kano, Sokoto, Kebbi har ma da Jihar Oyo su ka halarci taron. Ana dai kokarin ganin yadda Majalisun Jihohi za su kafa wannan dokar nan da ta kare hakkin kananan yarada kuma dabbaka ta.



Bukky Shonibare a wajen taron

Dokar za ta ba ‘ya ‘ya ‘yancin su auri wanda su ke so idan har sun girma sannan kuma a ba su ilmi mai inganci tare da haramta masu talla da yawan bara wanda hakan ke haifar da ‘da mara ido a al’umma.

An dai gayyaci manyan mutane inda suka gabatar da lacca da kasida game da batun. A mafi yawan Jihohin Arewa dai ba a kafa wannan doka da za ta ba yara ‘yancin su ba. Wanda ba shakka wannan na cikin abubuwan da ke maido mu baya kamar yadda Mawaki ya fada.



Taron karawa juna sani da YouthHubAfrica su ka gudanar a Kaduna


[NAIJ Hausa]

Wednesday, March 22, 2017

Tattalin arziki: Najeriya ta kama hanyar warwarewa-World Economist


Tattalin arziki: Najeriya ta kama hanyar warwarewa-World Economist




A wani nazari da World Economist tayi an bayyana cewa Najeriya ta fara fita daga matsalar tattalin arziki a wannan watan na Maris. Yanzu ma haka dai Dala na can tana shan mugun kashi a kasuwa. 

Tattalin arzikin Najeriya ya rugurguje a bara bayan dogon lokaci bai mots aba. Sai dai tun kwanaki wata Jami’ar Babban Bankin Duniya, Misis Eme Essien-Lore ta bayyana cewa Najeriya ta kama hanyar fita daga matsalar tattalin arziki.



Shugaba Buhari tare da Ministar kudi


Sai ga Jaridar World Economist ta Duniya tace a jiya Najeriya ta kama hanyar fita daga matsalar da ta shiga. World Economist ta Duniya a shafin ta tace abubuwa sun fara canza salo a kasar. Bayanan kasuwanci a kasar sun nuna cewa alkaluma na kara yin sama ne.

Tattalin arzikin Najeriya dai ya fara bunkasa bayan dogon lokaci babu wani cigaba. Hasashe da bincike na harkar kasuwanci ya kai maki 53.5 wanda shi ne mafi yawa da aka samu tun a shekarar bara.

Jaridar tace duk da cewa yayi wuri a ce ko an kama hanyar shawo kan tattalin arziki gaba daya amma fa canjin da aka samu ba shakka masu dorewa ne.


[NAIJ Hausa] 




Tuesday, March 21, 2017

Ko ka san wanene ya fi kowa kudi a Duniya?


Attajiri Bill Gates shi ya fi kowa kudi a Duniya


Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya


Bill Gates ya mallaki sama da Dala Biliyan 86




Kamar yadda aka saba a wannan shekarar ma dai kasurgumin Attajirin nan ne ya fi kowa kudi a Duniya. Arzikin Bill Gates ma dai karuwa yayi daga Dala Biliyan 75 zuwa Dala Biliyan 86 a bana. Mista Bill Gates shi yake da Kamfanin Microsoft.

Tun shekaru 23 da suka wuce kusan kowace shekara sai ka ga sunan Bill Gates a cikin manyan Attajiran Duniya. Yanzu haka dai shekara hudu kenan a jere babu wanda ya buge Bill Gates a Duniya.

A sahun farko na masu kudin Duniya bayan Bill Gate dai akwai irin su Warren Buffet, da kuma Jeff Bezos na Amazon. Sannan akwai  Amancia Ortega da Mark Zuckerberg mai shafin Facebook. Akwai sauran Attajirai irin su Carlos Slim Helu na kasar Mexico.


[NAIJ Hausa]

Abin da ya sa El-Rufa’i ya rubutawa Buhari wasika



Ashe Shugaba Buhari ne ya nemi El-Rufa’i ya rubuto masa takarda




Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’i ya rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari kwanaki inda ya fada masa cewa akwai gyara a tafiyar. Sai dai yanzu mun gano dalilin da ya Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wannan takarda

Kwanan nan aka samu labarin cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wata wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yake kiran sa da yayi maza yayi wasu gyara a mulkin sa, ciki dai ana bukata ya sallami wasu na kusa da shi irin su Abba Kyari da Babachir Lawal.



El-rufa'i lokacin da ya kai ziyara Daura wajen Buhari


Sai dai bincike da wata Jarida tayi an gano cewa ashe shugaba Buhari ne da kan sa ya nemi Malam Nasir El-Rufa’i ya rubuta wannan takarda a sa’ilin da su ka hadu a Garin Daura lokacin bikin Sallah a Satumban bara.

Dama can an yi taro da Kungiyar Arewar nan ta ACF inda suka nemi a fadawa Buhari cewa ya tsige Sakataren Gwamnatin sa da kuma Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnati. Haka kuma Gwamna El-Rufa’i ya rubuta cikin takardar ta sa bayan nazari.

Rahotannin sun nuna cewa wasu na kusa da shugaban kasar ne su ka fito da takardar Duniya ta gani domin a dauka cewa Gwamna El-Rufa’i yana yi wa Shugaba Buhari zagon kasa ne. Wasu dai na ganin cewa siyasar tana kadawa ta wajen Gwamnan na Jihar Kaduna kuma suke kokari su taka masa birki.




[NAIJ Hausa]

Wadanda suka fi kowa kudi a Najeriya


Mutane 3 da suka fi kowa kudi duk Najeriya



Alhaji Aliko Dangote shi ne mai kudin Najeriya da ma Afrika gaba daya


Mike Adenuga ne ke bayan Dangote a kasar nan


Ko kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?


1.      Aliko Dangote
Rahotanni da ke fitowa na wannan shekarar daga Mujallar Forbes sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya fita daga cikin sahun mutane 100 da suka fi kowa kudi a Duniya. Amma duk da haka shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf Nahiyar Afrika ba ma Najeriya ba. Dangote ya ba Dala Biliyan 12 baya.


2.      Mike Adenuga
Adenuga ne mai rike da kamfanin GLO kuma shi ne na biyu a bayan Dangote in dai kudi ake magana a Najeriya. Adenuga mai shekaru 63 ya mallaki sama da Dala Biliyan 5.8. Adenuga ne dai na 250 a cikin masu kudin Duniya.


3.      Folorunsho Alakija
Ina ka baro Folorunsho Alakija? Ka ji manyan mata! Ba ma Najeriya ba, duk Duniya da wuya a samu bakar mace da ta kera Alakija kudi. Shekarun baya dai ta zarce Attaajira Oprah Wimfrey ta Amurka. Alakija mai shekaru 66 ta tsunduma ne a harkar mai ta kuma mallaki sama da Dala Biliyan guda.



[NAIJ Hausa]

Monday, March 20, 2017

Allah yayi: Man Utd ta motsa bayan wata shida



Man Utd ta tashi daga na 6 bayan rabin shekara




Kungiyar Man Utd ta tashi daga mataki na 6 wanda ta dade a kai a wannan makon. Yanzu haka Man Utd ta dawo mataki na 5 inda ta kerewa Kungiyar Arsenal. Sai dai abubuwa na iya cabewa idan Man City da sauran manya suka ci wasannin su.

Man Utd dai tayi nasara ne bayan ta doke Kungiyar M/Boro da ci 3-1. Wannan ne kusan wasa na farko bayan Kungiyar M/Boro ta kori Kocin ta wanda tsohon Mataimakin Koci Jose Mourinho na Man Utd ne Aitor Karanka.

Marouane Fellaini da Dan wasa Smalling su ka jefa kwallaye a raga. Shi ma dai Dan wasa Jese Lingard ya zura kwallo mai kyau. Alvaro Negredo na Kungiyar Boro ne ya ci wa Kungiyar kwallo guda. Man Utd dai ta kai kusan watanni 6 a mataki na 6 a gasar firimiya.



Kocin Man Utd Jose Mourinho



[NAIJ Hausa]

Da gaske Dino Melaye bai gama A.B.U ba?


Ashe wani babban Sanata bai kammala makaranta ba?




Jaridar Sahara Reporters ta tasa wani Sanata a gaba inda tace ashe bai kammala Jami’ar ba. Sai dai Sanatan ya maida martani yace ayi a gaji a kyale sa

Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa Sanata Dino Melaye bai karasa karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba aka sallame sa. Sahara Reporters ta fitar da hotunan kwas-kwasan da Sanatan ya dauka inda aka nuna cewa ya fadi.

Sanatan ya mayar da martani inda yace sharri ne kurum ake masa. Melaye yace nan gaba ma ana iya cewa shi ba ‘Dan Najeriya bane. Sanata Melaye yace ba wannan bane karo na farko da Sahara Reporters tayi masa sharri.

Dino Melaye ya bayyana cewa yanzu haka yana karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariyar inda yake Digirin sa na 7. Sanatan yace a je a duba idan har karya ne a sa Magu na EFCC ya kama sa ya daure.



[NAIJ Hausa]

Sunday, March 19, 2017

Shugaban kasar Ghana ya nada Ministoci fiye da 100


Shugaban kasar Ghana ya kafa tarihi a kasar sa 


Sabon shugaban ya nada Ministoci 110


Jama’a dai na ta kuka game da wannan lamarin





Sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya nada Ministoci sama da 100 a Gwamnatin sa. Shugaban dai yayi alkawari zai rage kashe kudin da Gwamnati take yi sai kuma ga shi ya kara yawan Ministocin kasar wanda yace ya zama dole ne domin ayi gyara.

Shugaba Nana ya nada mataimakan Ministoci har 50 tare da Ministocin Jihohi guda 4 bayan kuma dai ga asalin manyan Ministoci har guda 56. Hakan dai na nufin Ghana na da Ministoci har 110 kenan a yanzu wanda ba a taba yin hakan ba a tarihi.

Jam’iyyar adawa dai ta soki wannan tsari inda kowane Minista yake da motoci da man fetur kyauta da kuma gida da masu gadi ga makudan albashi na akalla $4000 a kowane wata. Wasu Ma’aikatar dai akwai Ministoci har 5.

A Najeriya kuma Tsohon shugaban kasa Dr. Jonathan Goodluck yayi kira ga ‘yan siyasar kasar da su zama masu gaskiya a duk inda su ke. Jonathan yace masu rike da makamai su yi abin da ya dace na taimakon talakawa a lokacin da suke kan mulki.



[NAIJ Hausa]

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...