– Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra za tayi aure kwanan nan
– Zahra Buhari za ta auri dan Gidan hamshakin Attajirin nan, Muhammad Indimi
– Za a daura auren a farkon Watan Disamba Inji Kafofin yada labarai na zamani
Zahra Buhari tare da 'Angon' ta Ahmed M. Indimi
Ana
ta samun rahoto cewa Diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari za tayi aure nan da
kwanaki kadan masu zuwa. Zahra Buhari dai tayi fice ko a cikin ‘ya ‘yan
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Ana
ta yada cewa Zahra Buhari za ta auri Ahmed Indimi, dan hamshakin attajirin nan
na Maiduguri. Idan dai labarin ya tabbata, za ayi auren ne ba tare da wani
gawurtaccen biki ba. Ana cewa za ayi auren ne zuwa Farkon watan Disamban gobe.
Ahmed
Indimi dai yayi karatu ne a Turai, yanzu kuma shine Manajan Kamfanin ‘Oriental Energy Resources’. Ita kuma
Zahra, tayi karatu a Jami’ar Surrey da ke Ingila. Tana aiki a matsayin
Jakadiyar wata Kungiya mai suna SCAF masu cutar ‘sikila’
Kwanan
nan dai wata diyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta auri wani Alhaji Ya’u Kumo
dan Jihar Gombe. Ya’u Kumo tsohon ma’aikacin banki ne a Kasar. Alhaji Muhammad
Indimi dai yana cikin masu kudin Najeriya da kewaye.
A
can baya kuwa wata diyar Shugaba Muhammadu Buhari ta auri wani Babarbaren mai
suna Baba-Gana Sheriff. Da can dai an taba yada zancen cewa Zahra Buhari za ta
auri Gwamnan Zamfara, Abdul Aziz Yari.
Allah yasa alkhairi.
ReplyDeleteAllah yasa alkhairi.
ReplyDeleteAllah yasa alkhairi
ReplyDeleteAmeen
ReplyDeleteAn kasa abokina! Hahahaha
ReplyDeleteYou know your projects stand out of the herd. There is something special about them. It seems to me all of them are really brilliant! sa gamingsa gaming
ReplyDelete