Monday, November 21, 2016

An sa Ranar auren Zahra Buhari



Diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Zahra za tayi aure kwanan nan


Zahra Buhari za ta auri dan Gidan hamshakin Attajirin nan, Muhammad Indimi


Za a daura auren a farkon Watan Disamba Inji Kafofin yada labarai na zamani



 


Zahra Buhari tare da 'Angon'  ta Ahmed M. Indimi


Ana ta samun rahoto cewa Diyar Shugaban Kasa, Zahra Buhari za tayi aure nan da kwanaki kadan masu zuwa. Zahra Buhari dai tayi fice ko a cikin ‘ya ‘yan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. 

Ana ta yada cewa Zahra Buhari za ta auri Ahmed Indimi, dan hamshakin attajirin nan na Maiduguri. Idan dai labarin ya tabbata, za ayi auren ne ba tare da wani gawurtaccen biki ba. Ana cewa za ayi auren ne zuwa Farkon watan Disamban gobe.

Ahmed Indimi dai yayi karatu ne a Turai, yanzu kuma shine Manajan Kamfanin ‘Oriental Energy Resources’. Ita kuma Zahra, tayi karatu a Jami’ar Surrey da ke Ingila. Tana aiki a matsayin Jakadiyar wata Kungiya mai suna SCAF masu cutar ‘sikila

Kwanan nan dai wata diyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta auri wani Alhaji Ya’u Kumo dan Jihar Gombe. Ya’u Kumo tsohon ma’aikacin banki ne a Kasar. Alhaji Muhammad Indimi dai yana cikin masu kudin Najeriya da kewaye. 

A can baya kuwa wata diyar Shugaba Muhammadu Buhari ta auri wani Babarbaren mai suna Baba-Gana Sheriff. Da can dai an taba yada zancen cewa Zahra Buhari za ta auri Gwamnan Zamfara, Abdul Aziz Yari.

6 comments:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...