Sunday, November 13, 2016

Tashin Hankali: Bam ya kashe wani Gwamna


Harin Bam ya kashe wani Gwamna a Kasar Turkiyya
 

‘Yan ta’adda sun tada bam a Ofishin wani Gwamna a Kasar Turkiyya

‘Yan Sanda sun kama mutane da dama da ake zargi da wannan laifi

Wannan abu ya faru ne a Kudancin Kasar Turkiyya

 

Harin bam yayi sanadiyar mutuwar wani Gwamna a Kasar Turkiyya. Wannan mummunan abu ya faru ne a kwanan nan. Tuni dai Jami’an ‘Yan Sanda suka kama wadanda ake zargi har mutane 30. ‘Yan ta’addan sun tada bam din ne a Ofishin Gwamnan, hakan yayi sandaiyar mutuwar sa da wasu mutanen.

Kungiyar Matasa ta YPS ta Jam’iyyar Kabilar Kurdawa watau PKK sun dauki nauyin wannan aika-aika. An dai kai wannan hari ne a Ranar Alhamis da ta wuce a Garin Mardin da ke Kudancin Kasar na Turkiyya. Jaridar ANF mai kusa da ‘Yan ta’addan suka rahoto hakan.

A harin dai an rasa Gwamna Muhammad Fatih Safiturk na Yankin Derik. Ya samu mugayen rauni na kuna da bam din ya tashi, nan aka garzaya da shi asibitin da ke Birnin Gazientep ta helikwafta. Amma dai bai tashi ba, Jiya ya samu cikawa Inji Jaridar Dogan.
 
A Afrika kuwa, Rahotanni na nuna cewa Mayakan Boko Haram sun mika kawunan su da iyalan su, sun kuma ajiye makaman Yaki a Yankin Chad. ‘Yan Boko Haram din fiye da 240 suka ce wa Rundunar hadin gwiwa cewa ba su iyawa. A baya dai Boko Haram ta kashe mutane kimanin fadin Kasar Belgium ta Turai.

1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...