Wasu dalibai 'yan makarantar FGGC Oyo sun yi hadari a mota wajen dawowa gida hutu

Wata katuwar mota ta fado kan yara dalibai ‘Yan makaranta, inda ta
latse wasu daga cikin su har lahira. Wannan abin takaici ya faru ne a
hanyar dawowa gidan ‘yan makaranta domin hutun yada zango. Wannan
katuwar gingimari tana dauke ne da Garri, tayi sandiyar mutuwar dalibai
har guda hudu.
Wannan mummunan abu ya auka ne da dalibai ‘yan
makaranta Sakandare ta mata watau FGGC Oyo. An rasa dalibai hudu da kuma
direba daya a wannan mummunan hadari. The Nations ta rahoto cewa,
wannan hadari ya faru ne a Ranar Lahadi daidai karfe 3:30 na Yamma a
kusa da wata kasuwa da ke Garin Sabo da ke kusa da Garin Oyo.
Wata
gingimari dauke da Garin rogo ta fada kan daliban ne inda ta kashe guda
hudu nan take da kuma Direban motar. Daliban da suka rasa rayukan nasu
su ne; John Olubukola, Giwa Taibat, Ladipo Mojisolo, Ibirogba Maryam;
Daliban ‘Yan aji uku ne zuwa shida. Tuni dai aka bizne wadannan dalibai
cikin kuka da jimami.
Sai dai guda biyar sun samu damar tsira da ran su, tuni dai ‘Yan Sanda sun kama direban wannan babbar mota.
A karanta labarai a shafin NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment