Kuma
daina tunani zan dawo Inji Jonathan
– PDP ta tuna da Shugaba Jonathan, inda tace anyi Gwarzo
– Jiya Goodluck Jonathan ya cika shekaru 59 a duniya
– Jam’iyyar PDP tace Shugaba Buhari ba zai samu nasara wajen Yaki da cin hanci da rashawa a Kasar nan ba
Jam’iyyar PDP ta tuna da
Tsohon Shugaba Jonathan Goodluck yayin da ya cika shekaru 59 a jiya. Shugaban
Bangaren Jam’iyyar PDP din, Sanata Ahmad Makarfi yace Shugaba Jonathan din ba
karamin jan gwarzo bane.
PDP tace har yanzu ana shan
romon ayyukan da Shugaba Jonathan yayi wajen fannin tsarin mulki da siyasa,
ilmi, da kuma sauran hanyoyin more rayuwa. PDP tace Shugaba Jonathan yana cikin
wadanda suka mika mulki salin-alin a Nahiyar Afrika, ko don haka tauraruwar sa
ta ke kara haske a duniya.
Ana ta rade-radin cewa
Goodluck Jonathan din zai dawo, sai dai a shafin sa na kafar Facebook ya rubuta cewa shi fa ya tafi
kenan, sai labari. Shugaba Jonathan yace ai yanzu mulki kuma sai ‘ya ‘yan su da
jikoki, don su kam sun yi sun gama. Jonathan yace Kasa ai ba ta cigaba da
Tsofaffi a mulki.
Haka kuma, Jam’iyyar PDP mai
adawa a Kasar tace babu inda Shugaba Buhari zai kai wajen Yaki da cin hanci da
rashawa a Kasar nan domin ya saka son kai a lamarin.
[NAIJ Hausa]
Chan gasu gada
ReplyDelete