Sunday, November 13, 2016

Jihar Edo: An yi sabon Gwamna



Gwamna Oshiomole ya sauka daga Gwamnan Jihar Edo

A jiya aka nada Mista Godwin Obaseki a matsayin sabon Gwamna na Jihar Edo

 


Wa’adin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya kare

 


Sabon Gwamna Obaseki ya yabawa mai barin-gado Adams Oshiomole yace anyi namiji

 

A jiya Asabar aka nada Sabon Gwamna a Jihar Edo. Mista Godwin N. Obaseki ya zama Sabon Gwamna na Jihar bayan wa’adin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya kare. Gwamna Obaseki ya yabawa Kwamared Adams Oshiomole da irin ayyukan da ya zuba a Jihar.

Obaseki yace Gwamna mai-barin-gado Adams Oshiomole yayi namijin kokari wajen ganin ya canza Jihar Edo. Babban Alkalin Jihar, Alkali Cronwell Idanosa ya rantsar da Gwamnan, Godwin Obaseki da kuma Mataimakin Sa, Phillip Shu’aibu. 



Mutane da dama sun halarci taron rantsar da sabon Gwamnan, Tsohon Shugaban Kasa Yakubu Gowon na wajen taron. Haka Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki da kuma Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Cif John Oyegun. Kai ba a bar manyan ‘Yan kasuwa irinsu Alhaji Aliko Dangote a baya ba.

Sabon Gwamna Obaseki yayi alkawarin cigaba da duk ayyukan da Tsohon Gwamna Oshiomole ya fara, ya kuma yi alkwarin samar da ayyuka 200, 000 cikin wa’adin shekara hudu. Sabon Gwamna Obaseki yace zai rike noma da harkar kasuwanci a Jihar. Obaseki yace zai dauki harkar karatun mata da lafiyar su da muhimmanci. Ya kuma kira ‘Yan adawa da a zo a hada kai.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...