Thursday, November 17, 2016

Ka ji abin da Femi Fani-Kayode ya fada game da Shugaba Buhari


Donald Trump ba zai kyale Shugaba Buhari yayi abin da yake so ba-FFK


Femi Fani Kayode yace Shugaba Buhari na nema ya musuluntar da Najeriya

 

Tsohon Ministan Kasar nan, Femi Fani-Kayode yace gara da Donald Trump ya lashe zaben Kasar Amurka


FFK yake cewa Sabon Shugaban Kasar Amurka ba zai bar Shugaba Buhari ya musuluntar da Kasar nan ba


Kayode ya taya Trump murna bayan ya fito daga tsari 

 

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama na Kasar nan, Femi Fani-Kayode ya fito daga tsari kwanan nan. Bayan fitowar sa, ya taya Sabon Shugaban Kasar Amurka da aka zaba, Donald Trump murnar lashe zaben Kasar. Yace gara da Trump din ya kada Clinton.

Ko can dai Mista Kayode ya dade yana goyon bayan Trump, ya taba wani rubutu a nan mai suna ‘Trump da kuma Musulunci’ inda yake cewa hamshakin Dan kasuwan nan Donald Trump, zai lashe zaben Jam’iyyar sa ta Republican, kana kuma ya lashe zaben Kasar Amurka inda za su kara da Hillary Clinton. 

A wancan lokaci FFK yace: ‘Duk da cewa mutane da dama ba za su yarda da ni ba har a Najeriya, amma na tababa cewa Trump zai lashe zaben Amerika, kuma ina tare da shi. Mu (Yan Najeriya) abin da muke so.'

Femi Fani-Kayode yace Trump ba zai kyale a musuluntar da wata Kasa ba ko ya bar masu tsantsenin ra’ayin addini suna abin da suka ga dama. Kayode yace Trump ne maganin Shugaba Buhari. Femi Fani-Kayode yake kuma cewa Sabon Shugaban ba zai bari a ci gaba da keta hakkin bil adama ba

Kwanan nan ne dai Femi Fani Kayode ya fito daga Gidan tsari na Kuje, inda ya ce ya gana da Nnamdi Kanu da wasu 'Yan 'Boko Haram'. Da fitowar sa dai ya cigaba da sukar Gwamnatin Muhammadu Buhari kamar yadda ya saba.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...