Monday, November 21, 2016

An kai hari gidan Mamman Daura


‘Yan bindiga sun sace wani Tsohon Ministan Najeriya jiya a Garin Kaduna

Wasu ‘Yan bindiga ne suka yi gaba da Ambasada Bagudu Hirse

An kai wannan hari ne a Gidan Mamman Daura da ke Garin Kaduna

 

 

'Yan bindiga sun sace Ambasada Bagudu Hirse a gaban Gidan Mamman Daura

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sace wani Tsohon Ministan Kasar nan a Gidan Alhaji Mamman Daura da ke Garin Kaduna. Wasu ‘Yan bindiga ne dai da ba a san su ba, suka sace Tsohon Ministan harkokin waje na Kasar, Ambasada Bagudu Hirse.

Wannan abu ya faru ne dai jiya a gaban Gidan Alhaji Mamman Daura da ke kan Titin Inuwa Wada a cikin Garin Kaduna. Ana zargin cewa Alhaji Mamman Daura yana gida a lokacin da wannan abu ya faru. An ce ko a lokacin yana karbar ziyara daga ‘Yan uwa da abokan arziki. 

Tsohon Ministan dai ya zo Garin ne domin ta’aziyar rashin Marigayi Ibrahim Dasuki, tsohon Sarkin Musulmi. Gidan Marigayi Dasuki bai da nisa da Gidan Alhaji Mamman Daura, don haka ne Ambasadan ya tsaya don ya gaida Mamman Daura. 

Wanda abin ya faru a gaban sa, yace bayan Alhaji Bagudu ya fito daga mota tare da wani abokin sa, sai wasu mutane kwatsam suka keto a guje a mota kirar Toyoto Corollo sun sha damara, Nan-take suka ce ya shiga motar su, ko da ya tsaya wata-wata, sai suka harba bindiga, tuni kowa ya tsere. Yanzu haka dai ba a san inda suka yi da shi ba. Jihar Kaduna dai ta zama abin da ta zama game da harkar rashin tsaro.

Sai dai wata majiya ta nuna cewa an kai harin ne ga Abba Kyari, wanda shine Shugaban Ma'ikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, wanda na kusa da Alhaji Mamman Daura ne, kuma ake sa ran yana gidan a lokacin. Ana dai zargin su Mamman Daura sun rike madafan iko na Gwamantin Shugaba Buhari. 



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...