Wednesday, November 9, 2016

Donald Trump ya kerewa Hillary Clinton a zaben Amurka


– Dan takara Donald Trump yayi wa Hillary Clinton gaba Inji Gidan BBC


Trump dan takarar Jam’iyyar Republican ya buge ‘Yar takarar Democrat Hillary Clinton a zaben wani Yanki


Ana zaben sabon Shugaban Kasa a Amurka 

 



Rahotannin zabe daga Gidan BBC na cewa Donald Trump na kan gaba a zaben wasu Yanki na Kasar Amurka. BBC ta ce Trump ne gaba a kuri’u na wasu Jihohin Kasar da ka iya yin tasiri a zaben. Ana tunanin irin wadannan Jihohin ne za suyi tasiri wajen zaben Sabon Shugaban Kasar na Amurka.

Dan takara Donald Trump; wanda ya saba kawo rikici ya samu nasara a Jihohin Florida, Ohio da kuma Carolina ta Arewa. Ita kuma Misis Hillary Clinton ta kawo Virginia. Sannan kuma ana kusa da gane wanda yayi nasara a Pennslyvania; wanda yanzu ana kusan daf-da-daf. BBC tace Donald Trump ya ci Utah, Alabama, Indiana, Texas, Kansas, dsr.

A Garin Michigan kuwa, inda Jam’iyyar su Clinton ke da karfi, shima ana kunnen-doki tsakanin ‘Yan takaran. Rabon da Mutanen Michigan su zabi Dan Jam’iyyar Republican tun shekaru kusan 30 da suka wuce. Hillary Clinton ce gaba California, New York, New Jersey, Illinois, Colarado, New Mexico, Washington, dsr.

Donald Trump ya bayyana cewa yayi farin cikin lashe Garin Ohio, wanda tun lokacin Shugaba Bush ba su kara zaben dan Jam’iyyar Republican ba. Donald Trump ya buge Clinton a Yankunan Kudu, ita kuma tayi nasara a Yankin Arewa maso yamma. Yanzu haka har dala ta fara fadi saboda nasarar da Trump ke samu.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...