– Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa,
Atiku Abubakar yace su El-Rufai mayaudara ne
– Malam Nasir El-Rufai ya mayar da martani, inda yace Atiku Abubakar makaryaci ne
– Gwamna El-Rufai yace Atiku na harin zaben 2019 ne
Rikici na ta kara kamari a
cikin Jam’iyyar APC tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da Malam Nasir El-Rufai.
Alhaji Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar nan ya bayyana cewa
Malam Nasir El-Rufai da Nuhu Ribadu sun ci amanar sa. Sai dai Malam Nasir
El-Rufai ya fito ya kare kan sa.
Malam Nasir El-Rufai wanda
shine Gwamnan Jihar Kaduna, yace Atiku Abubakar din karya yake yi. El-Rufai
yace Atiku na neman ci masa mutunci ne kurum. Atiku Abubakar ya bayyana cewa
shi bait aba satar kudi ba lokacin yana Gwamnati, yace asali ma su Nasir
El-Rufai suka yi kokarin masa tayin hakan, shi kuwa yace sam bai dace ba.
Atiku Abubakar yace El-Rufai
yayi kokarin ba Atiku hannun jari daga Kamfanin Transcorp, inda shi kuma ya ki karba. Shi kuma Malam Nasir El-Rufai
yace lallai Atiku makaryaci ne. El-Rufai yace shi bai karbi hannun jari a
Kamfanin ba, shine zai ba wani? El-Rufai dai ya tona asirin duk abin da ya faru
a littafin sa, ya kuma ce duk yakin neman zabe ne ake yi.
Turakin Adamawa ya rike
Mataimakin Shugaban Kasar nan na shekaru takwas, lokacin Shugaba Obasanjo.
Alhaji Atiku Abubakar din ba da Dan Siyasa ne kadai ba, hamshakin dan kasuwa
ne. Atiku dai yace bai taba satar kudi ba.
A karanta shafin NAIJ Hausa
malam kenan!
ReplyDeleteKa san Malamai da gaskiya.
Delete