Atiku Abubakar yace bai taba satar kudi ba...
Kai makaryaci ne...-El Rufai
– Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar yace shi ba barawo bane
– Atiku Abubakar yace El-Rufai mayaudari ne
– Sai dai Malam Nasiru El Rufai yace karya Atiku yake yi, idan ba tsoro ba, ya je Amurka mana
Alhaji Atiku Abubakar,
Turakin Adamawa ya rike Mataimakin Shugaban Kasar nan na shekaru takwas,
lokacin Shugaba Obasanjo. Alhaji Atiku Abubakar din ba da Dan Siyasa ne,
hamshakin dan kasuwa ne. Atiku yace shi bai saci kudi ba game da wani sabon
zargi da ake yi masa.
A wata hira da Alhaji Atiku
Abubakar yayi da Mujallar Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a
Najeriya yace shi fa bai saci kudin kowa ba. Atiku Abubakar yace sharin da ake
masa shine ya nada wasu Ministoci a lokacin Gwamnatin Obasanjo, Atiku Abubakar
yace in dai wannan ne, ya wanke kan sa a Kotu.
Atiku Abubakar yace Kotu ta
wanke sa sarai, don haka babu wanda ya taba samun sa da laifin sata a Kasar
nan. Atiku Abubakar yace duk rikicin siyasa ne kurum ke kawo wannan maganganu.
A littafin da Malam El Rufai ya rubuta, ya zargi Atiku Abubakar da laifuffuka
na awon gaba da kudi, sai dai Atiku Abubakar din yace Nasir El Rufai bai kawo
wata hujja ba.
Atiku Abubakar yace shi Malam
Nasir El Rufai ne ma yayi kokarin kawo masa wasu hannun jari don ya karba, shi kuwa yace bai dace
ba. Gwamna El-Rufai ya mayar da martani inda yace Atiku ya saba karya, idan kuma ya isa ya shiga Kasar Amurka idan ba a kama sa ba.
No comments:
Post a Comment