Tuesday, November 29, 2016

Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai 11,000

An yaye daliban ABU Zaria


Jami’ar ABU Zaria ta yaye dalibai sama da 11,000 a karshen wannan makon

 


Jami’ar ta yaye dalibai masu digiri da digirgir har ma da digir-digir

 


Ciki an samu guda 49 da suka ciri tuta

 

 Shugaban Jami'a, Farfesa Ibrahim Garba

Jami’ar Ahmadu Bello watau ABU Zaria ta yaye dalibai a karshen wannan makon. Jami’ar da ita ce ta farko a Arewacin Najeriya ta yaye dalibai masu digiri guda 11, 731. 

Kamar yadda muka samu labari akwai guda 2, 697 masu shaidar Digiri na biyu, sannan kuma guda 289 sun kammala karatun Digiri na uku watau Dakta. Ciki akwai guda  49 da suka ciri tuta, inda suka samu gamawa da mataki na farko watau 'first class'.

Shugaba Buhari ya ce za ayi bincike game da irin badakalar da ake samu a cikin Jami’o’i. Shugaban Kasar ya kuma yi kira da Jami’ar ta ABU Zaria da ta maida hankali wajen nazari game da harkar noma. Farfesa Rasheed na Hukumar NUC ne ya wakilci Shugaban Kasar. 

Shugaban Jami’ar Farfesa Ibrahim Garba ya bayyana irin cigaban da Jami’ar ta samu wajen fanni dabam-dabam a karkashin Shugabancin sa. ABU Zaria ta gina matatar man fetur, sannan kuma ta gano wani maganin cutar malaria na ciwon sauro.

Farfesa Garba ya kira daliban da aka yaye su zama masu tarbiya bayan ilmin da suka samu. Yanzu haka Jami'ar ABU Zaria ta yaye dalibai da dama a fadin duniya. Wannan ne dai karo na 39 da Jami'ar ta yaye daliban nata.




Muhammad Malumfashi daga Zaria
NAIJ Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...