Monday, November 28, 2016

Ashe dama tusa na magani?

Tusa na maganin cutar tsufa
 

Bincike ya nuna cewa tusa na maganin cututtuka da dama

 


Turawa sun gudanar da wani bincike inda suka gano cewa tusa na maganin cututtukan tusfa

 


Iskar tusa tana rage kamuwa da cutar hawan jini da ire-iren su


A wani sabon bincike na kwanan nan, an gano cewa tusa na magani na cututtuka kala-kala. A baya dai ana tunanin cewa iskar tusa na da mugun illa, sai dai yanzu nazari ya nuna ashe ba haka abin yake ba. Tusa na maganin cuta duk da mafi yawan tusa, sai ka ji ta da dan-karan wari.

Masana sun gano cewa a duk lokacin da kayi tusa, ka kuma shaki iskar, to tana da amfani a jikin Dan Adam. Iskar tusa na hana kamuwa da cutar dementia ta tsufa. Cutar dementia na sa yawan mantuwa da dimuwa ga tsofaffi. Idan ana shakar warin tusa, wannan cuta ba za ta kama mutum ba. 

Wasu Turawan Birtaniya ne dai suka gano cewa, tusa na dauke da Iskar Hydrogen Sulphate. Masana kimiyya sun ce wannan iskar na da amfani a jiki mutum, musamman a kwakwalwa. Hydrogen Sulphate na karawa kwakwalwa karfi kuma tana kare mutum daga cutar tsufa. 


Muhammad Malumfashi ya fassara
NAIJ Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...