Wasu
‘Yan Najeriya 27,500 sun shiga Kasar Italiya a sace
– ‘Yan Kasar Najeriya da dama sun isa Kasar Italiya ta barauniyar hanya
– Mutane fiye da 27, 500 suka kaura zuwa Kasar Italiya ta teku
– Da dama dai sun mutu a kan hanyar su zuwa can a halin yanzu
A cikin watan Jiya na Oktoba
kadai, mutanen Najeriya da Kasar Eriteria fiye da 27,500 su ka shiga Kasar
Italiya ta barauniyar hanya. Hukumar Turai mai lura da kan iyaka da ake kira
Frontex ta bayyana haka.
Hukumar tace ba a taba samun
irin wannan cin-ci-rindo ba haka a cikin lokaci guda. A ce a cikin wata guda
kusan mutum 30,000 sun kaura zuwa Kasar ba tare da an sani ba. Da yiwuwar
saboda kyawun yanayin ne jama’an wadannan Kasashe suka yi kaura zuwa Kasar ta
Italiya domin kuwa lokacin da sanyi zai yi kamari, zai yi wuya a iya
tsallakowa.
Mafi yawan masu hijiran dai
‘Yan Najeriya ne da kuma Kasar Eritrea. Sai dai an samu babbar matsala wajen
haurowa, mutane fiye da 127 aka samu sun mutu a hanya garin tsallake teku.
Mafi yawan ‘Yan Najeriya da
sauran ‘Yan Afrika da ke shiga Kasashen dai wahalar rayuwa ce ke kai su.
No comments:
Post a Comment