– Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana kokarin ta na ganin Jihar ta samu wadataccen abinci
– Gwamna Ambode yace suna hada kai da wasu Jihohi wajen ganin ba a bar Legas a baya ba
– Yanzu haka dai farashin man fetur yayi kasa, hakan ta sa ake ta fama a Kasar
Gwamnatin Jihar Legas ta
Gwamna Ambode na kokarin ganin yadda Jihar za ta samu wadataccen abinci. Wasu
Jihohin Kasar dai na fama da yadda za su biya albashi tun bayan da farashin man
fetur ya ragu a duniya. Shi kuma Gwamna Ambode yana kokarin ganin yadda abinci
zai samu ne a Jihar sa.
Gwamna Ambode ya bayyana
cewa a duk rana ana cin abinci na sama da Naira Biliyan uku a Legas. Don haka
ne Gwamna Ambode yace Legas ta shiryawa duk wanda zai zo kasuwancin kayan noma
a Jihar. Gwamna Ambode yace ba dalili ace Najeriya tana shigo da kayan abinci a
wannan lokaci.
Gwamna Ambode yayi wani taro
tare da Alhaji Sani Dangote da sauran manyan masu kasuwancin kayan abinci.
Taken taron dai ya kunsa yadda Legas za ta wadatu ne da abinci. Gwamna Ambode
yace Jihar sa ta hada kai da Kebbi wajen noman shinkafa da su masara. Ambode
yace tana nan kawai Jihar Legas za ta samu duk abincin da za ta ci.
Haka ma dai Audu Ogbeh yace
Gwamnatin Tarayya za ta shigo da manyan kayan aikin shinkafa wanda za su
taimaka wajen ganin Kasar ta noma shinkafa da za ta ci da kan ta nan da shekaru
biyu masu zuwa. Ministan noma yace Gwamnatin Tarayya za ta kawo manyan
na’urorin casar shinkafa guda 40 cikin Kasar.
Gwamna Ambode yace Jihar Legas ta nemi filin noma a Garuruwa irin su
Ogun, Oyo, da Abuja domin noman shinkafa da su kwakwan manja.
No comments:
Post a Comment