– Yau mako biyu kenan ba a san inda Gwamna Yahaya Bello na Kogi ya shiga ba
– Jama’a sun shiga wani hali, an rasa inda Gwamna ya shiga, ana tunanin ba sa da lafiya ne
– Kakakin Gwamnan yace ka da kowa ya tada hankalin sa, Gwamna na nan
A Jihar Kogi dai ana cikin
wani hali yanzu haka, don an rasa inda Gwamna Yahaya Bello na Jihar ya shige.
Yanzu makonni biyu kenan ba a san inda Gwamna na Jihar yake ba.
Wasu dai na ta rade-radin cewa Gwamnan ba sa da lafiya ne.
Har yanzu dai ba a bayyanawa
‘Yan Kasar inda Gwamnan ya shiga ba, Jaridar Daily Times tace ana tunanin
Gwamnan ya wuce wata Kasar ne waje domin rashin lafiya da ke damun sa. An ce
dai Gwamna Yahaya Bello ya bar aikin Jihar ne ga mataimakin sa, Simon Achuba,
wanda ba abin da yake sai karbar baki.
Yanzu haka dai abubuwa na
sha’anin mulki sun tsaya cak a Jihar na Kogi tun tafiyar Gwamnan. Sai dai
Kakakin Gwamna Yahaya Bello, Kingsley Fanwo yace duk karyar banza ce ake
yadawa. Mista Fanwo yace masu yada wannan jita-jita makiyan Jihar Kogi ne.
Mai magana da bakin Gwamna
Yahaya Bello, yace Gwamna na nan lafiya kalau babu abin da ke damun sa, yace
Gwamnan dai ya tafi hutu ne na mako biyu, kuma zai dawo aiki mako mai zuwa.
No comments:
Post a Comment