Sunday, November 13, 2016

Shugaba Buhari yayi farin ciki bayan Super Eagles sun ci wasa


Shugaba Buhari yayi farin ciki bayan da Kungiyar Super Eagles ta ci wasan ta

 


Shugaban Kasar, Muhammadu Buhari ya aika sakon jinjina ga ‘Yan kwallon kafar Kasar

 


Shugaba Buhari ya godewa Jihar Akwa Ibom da sauran ‘Yan kallo

 


Shugaba Buhari yayi farin cikin ganin Kungiyar Kwallon Kafar Super Eagles tayi nasara a wasan ta da ta buga jiya. Super Eagles na Najeriya sun doke Kasar Algeria da ci 3-1 a wasan zuwa cin Kofin duniya na shekarar 2018 a Kasar Russia.

Shugaba Buhari ya aika wannan sako ne ta daya daga cikin masu ba sa shawara game da harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina. Shugaba Buhari yace ‘Yan Super Eagles din ba su ba da kunya ba. Shugaba Buhari ya tabbatarwa Kungiyar Kwallon Kafan Kasar masu maki shida a zagayen, cewa mutanen Kasar na goyon bayan su dari-bisa-dari.

Shugaba Buhari ya kuma mika godiyar sa ga Gwamnatin Jihar Akwa Ibom inda aka buga wasan. An doka wasan ne a filin wasa na Godswil Akpabio da ke Birnin Uyo na Jihar. Shugaba Buhari ya kuma godewa ‘Yan kallo da magoya bayan Kungiyar.

Kasar Najeriya ta doke Kasar Algeria ne da ci 3-1, ‘Yan wasan Kungiyar Chelsea; Victor Moses da Kyaftin Mikel Obi suka ci kwallayen. Victor Moses ya zuba kwallaye har biyu a wasan. Yanzu Kasar Najeriya ce a kan gaba a rukunin na ta na zuwa Gasar cin kofin duniya da za a buga a Kasar Russia.




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...