– Kotu a Abuja ta kama wani mai gadi yayi sata
– Kotun da ke Ubguwar Area I a Birnin Tarayya ta bada belin wanda ake zargi

Wani Kotu da ke zama a
Unguwar Karmo da ke Area 1 a Babban Birnin Tarayya Abuja, ta bada belin wani
saurayi da ake zargi da laifin yayi sata. Ana zargin wannan saurayi da bai wuce
shekaru 19 ba ya sace kayan ginin gidan da yake gadi a Garin na Abuja.
Alkalin Kotun na Area 1,
Abubakar Sadiq ya bada belin wannan mai gadi mai suna Peter Gwaza Inji Jaridar
Daily Trust. An bada belin na sa ne a kan kudi har N500,000 tare da kawo wanda
zai tsaya masa.
Kotun tace dole wanda zai
tsayawa wannan mai gadi da ake zargi da lafin sata ya zama ma’aikacin Gwamnati,
kuma wanda yake akalla mataki na 7 na aiki. Yanzu haka dai an daga shari’ar
zuwa 10 ga wannan wata. An bayyana cewa dai wanda ake zargi ya bayyana cewa ya
saci kayan da ake magana, har ma ya sayar da su tuni kan kudi N17,000.
Ku karanta cikakkun labarai a shafin NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment