– Kungiyar 'Kaduna Project' ta Zariya ta karrama Sakataren Hukumar NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed
– Yariman Zazzau, Mannir Jafaru ya basa kyautar jinjina
– An nemi Shugaban NUC din da ya rike gaskiya da adalci
A wani taro da Kungiyar Kaduna Project ta gudanar, Kungiyar ta karrama sabon Sakataren Hukumar NUC ta kuma
taya sa murna. An kuma kira sabon Sakataren Hukumar NUC din da ya zama mai
gaskiya da adalci.
Kungiyar ta Kaduna Project da ta ke kamar
cibiya ta Musulunci, ta taya Farfesa Abubakar Rasheed murnar samun wannan
matsayi na Shugaban NUC. Kungiyar ta kuma taya Farfesa Umar Ibrahim murnar nada sa
Shugaban laburare na Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. A taron kuma dai, an
karrama Shugaban Asibitin Koyon aiki na Jami’ar da ke Shika, an kira
Shugabannin da suyi kokarin rike amana.
An taya 'Ya 'yan Jihar murna da kuma neman su da su zama masu gaskiya da rikon amana. Farfesa
Rasheed wanda asalin ‘Dan Garin Makarfi ne na Jihar Kaduna, ya zama Shugaban
Hukumar NUC mai kula da Jami’o’in Kasar nan a watan Agusta. Farfesa Rasheed
tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne.
Shugaban Kungiyar NIC,
Amir Muhammad D. Muhammad ya kira Farfesa Rasheed ya rike gaskiya da amanar al’umma,
ya zama mai amfani da basirar sa, ya kuma san cewa Ubangiji zai tambaye sa a
Ranar Kiyama.
Farfesa Rasheed tare da Yariman Zazzau, Alhaji Mannir Jafaru da Uban Taro Alhaji Falalu Bello, Dan Masanin Zazzau
Farfesa Abubakar Adamu
Rasheed yayi godiya ya kuma tabbatar da kamanta gaskiya a duk inda yake. Sauran
wadanda suka halarci taron sun hada da Mai Girma Yariman Zazzau, Mannir Jafaru
da kuma Dan Masanin Zazzau, Falalu Bello da Farfesa Abubakar Sani Sambo da kuma
wasu Manyan Malaman Jami’a da Shugabannin Al’umma.
Muhammad Malumfashi daga Zaria
NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment