– Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano yayi alkawarin taimakawa kasuwar kwadi a Jihar Kano
– Masu kwadi suna cin Karen su ba babbaka a Jihar Kano
– Jama’a da dama yanzu an ganewa naman kwadi

Dr. Abdullahi Umar Ganduje,
Gwamnan Jihar Kano ya tabbatar da cewa Gwamnatin sa za ta taimakawa masu harkar
naman kwadi a Jihar Kano. Jaridar Premium Times ta gano cewa dai yanzu naman
kwadi sun zama abin da suka zama.
Masu kwadi a Jihar Kano dai
da ma wasu Yanki na Arewacin Kasar suna cin Karen su ba tare da babbaka ba a
halin yanzu, don kuwa mutane da dama yanzu sun ganewa naman kwadi a Kasar nan.
Yanzu haka, an gano wata kasuwa a Kadawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam a
Jihar Kano da ke da kasuwar kwadi.
Yanzu haka dai ‘Yan kasuwa
da dama sun shiga wannan Gari na Garun Malam domin wannan kasuwanci na gyara
naman kwadi. Ko dama can dai ba yau aka fara harkar gyara naman kwadi ba inji
masu abin. Wani dan kasuwan yace ana sayar da guda daya kusan N200.
No comments:
Post a Comment