Thursday, November 17, 2016

An kona wani yar da don ya saci Garin Rogo

Ashe ‘Yan Najeriya ba su da imani?



An kona wani karamin yaro kurmus a Legas wai don ya saci Garin Rogo


Yaron dai bai wuce shekara 7 ba a duniya


Wasu ‘Yan Najeriya suna ganin duk laifin Shugaba Buhari ne

 

 

A Garin Legas ma wani mummunan abu ya faru kwanan nan, inda wani sabon bidiyo ya bayyana. Idan dai ta tabbata, wasu’Yan Najeriya suka kona wani yaro karami dan shekara 7 har ya mutu don ya saci Garin rogo.

Wani daga cikin wanda abin ya faru a gaban sa, ya dauki bidiyo. Babu dai wanda yayi kokarin agazawa yaron kar a kashe shi,  haka dai yayi ta konewa har ya isa lahira. Ana zargin yaron da satar Garin rogo ne dai, hakan ta sa mutane suka dauki doko a hannun su.

Sai dai wasu ‘Yan Najeriya suna ganin cewa duk Shugaba Buhari ya jawo wannan hali da ake ciki. Masu amfani da hanyoyin sadarwa na zamani na Facebook da Twitter suka ce duk yunwar da Shugaba Buhari ya jefa Kasar ne ya kai ga wannan.

Yanzu haka dai ana neman Jami’an ‘Yan Sanda suyi bincike domin gano wadanda suka yi wannan aiki su hukunta su. Ba yau dai 'Yan Najeriya suka fara daukar doka a hannun su ba, manyan barayi kuma sai yadda suka ce za ayi.




1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...