Tun daga Kaduna, wani mutumi zai yi tattaki zuwa Birtaniya
– Wani mutumi zai yi tattaki daga Garin Kaduna zuwa Kasar Birtaniya
– Wannan mutumi ya fara tafiyar ne Ranar Lahadi 20 ga wannan wata
– Wannan mutumi zai yi wani tattaki ne domin jawo hankalin mutanen duniya game da ta’addanci
Wani
mutumi ya kama shirin tattaki daga Garin Kaduna, kuma ba zai tsaya ko ina ba
sai Kasar Ingila. Wannan mutumi zai yi wannan tafiya ne a kafa saboda ya jawo
hankalin mutanen Duniya game da harkar ta’addanci.
Wannan
matafiyi mai suna Abubakar Duduwule zai bi ta Jihar Neje ne, daga nan sai Garin
Abuja, shikenan sai ya zarce har Kasar Birtaniya, inda zai tsaya. Kuma dai zai
yi wannan tafiya ne duk a kafa.
Duduwule
yace ya zagaye kaf Arewa yana yada zaman lafiya da rashin fitina da kuma illar
shaye-shaye. Yace ya kamata yanzu ya shiga Duniya. Abubakar Duduwule yace tun
shekarar 2008 ya fara irin wannan tattaki.
Shekarun
baya dai Abubakar Duduwule ya ja kafa har Kasar Kamaru daga Jihar Adamawa.
Duduwule dai yana kokarin yada sakon yaki da ta’addanci a ne a duniya, hakan ta
sa zai taka da kafar sa har Kasar Birtaniya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment