Friday, November 4, 2016

Ashe da gaske tusa na hura wuta?



Tusa ta kona wata mata


Ashe da gaske ne da ake cewa tusa na hura wuta, yau tusa ta tada wuta
 



Abin mamaki; wata mata tayi tusa yayin da ake yi mata aiki asibiti, hakan kuwa ta jawo gobara
 



Iskar tusa ta hade da kayan aikin wuta a asibiti, hakan ya sa wannan mata ta kone

 

Abin mamaki; Malam Bahaushe yayi gaskiya, ashe da gaske ne da ake cewa tusa na hura wuta, yau tusa ta tada wuta ma ba hura ta ba. A Kasar Japan wani abin mamaki ya faru a wani asibiti, inda tusa ta tada wuta yayin da ake wani aiki. Likitoci kawai sai suka ga wuta na tashi ana tsakiyar fede wannan mata a asibiti.

Wannan abu ya faru ne a Kasar Japan, a wani Asibitin koyon aiki da ke Tokyo. Likitoci suna tsakiyar fede wata mata da na’urar Laser mai kamar wakilya, sai gobara ta barke, kuma ba wani abu ne ya jawo gobarar ba sai tusar da matar tayi yayin da ake yi mata aiki, kamar yadda bincike ya nuna.


An dai samu matsala ne lokacin da wannan mata da ake yi wa aiki ta saki tusa, iskar tusar ta sa wuta ta tashi a nan take. Su kan su likitocin da fari, sun rasa gane abin da ya faru. Sinadarin da ke cikin tusar ta hade da na’urar Laser, wannan ya sa wuta ta kama. 

Wannan abu ya jawo wannan mata mai shekaru 30 ta kone a kafafun ta da kewayen kugun ta. Dama can ana mata aiki ne a mahaifar ta. Sa'alin da abin ya faru, kimanin watanni uku da suka wuce, ba a gane abin da kawo gobarar ba, sai da aka yi dogon bincike sai aka gane ashe dai tusa na hura wuta.




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...