Wednesday, November 9, 2016

Abubuwa 5 da suka sa Trump ya doke Clinton

ZABEN AMURKA: DALILAN DA SUKA SA DONALD TRUMP YAYI NASARA

Tun daga farkon tafiyar, Donald Trump ya ba mutane mamaki, babu wanda ya taba tunanin zai tsaya takara, ina ma kuma ace ya ci tikitin Jam’iyyar Republican, yau kamar wasa Trump zai zama Shugaban Kasar Amurka na 45 a Tarihi. Mutumin da bai taba rike ko cokali a Gwamnati ba, ya zama Shugaban Kasa, kuma Kasa irin Amurka. 

Anthony Zurcher ya bayyana wasu dalilali da suka sa Donald Trump yayi nasara a zaben na Kasar Amurka. Ga su kamar haka: 



Kuri’un Bakaken fata
Donald Trump yayi nasara a Garuruwan da kuri’un bakaken fata ke da dama, irin su; Ohio, Florida, da North Carolina. Wadannan Garuruwa, asalin su tun fil azal Jam’iyyar Democrat suke yi, wannan karo, Trump da Jam’iyyar sa, sun yi nasara. Fararen fatar da ke irin wannan Yanki musamman marasa karatu sun fito kwan su-da-kwarwatar su wajen ganin Trump yayi nasara.
Mutanen Virgina, Colarado, da Wisconsin sun ba Clinton mamaki da kunya, duk ta cewa ta ci sauran Yankin da bakaken fata ke da galaba, irin su: Birnin New York da California, Bakaken da ke Jihar Utah sun kada ta. Dama can wasu musamman ‘Yan karkara suna ganin Shugaba Obama bai tsinana masu komai ba a shekara 8.

Trump bare ne
Hillary ba yau ta saba shiga Gwamnati ba, asali ma Mijin ta ya taba Shugabancin Kasar Amurka. Ita da kan ta ta taba neman takara, ta kuma rike Sakatariyar Gwamnati. Don haka sune manyan Kasar, an dade ana damawa da su, ba yau ta shigo ba. Shi kuwa, Trump, kasuwancin sa kurum ya sa gaba, bai taba siyasa ba ko shiga cikin Gwamnati. Wannan ya sa wadanda ba su son zaben mala’u, suka bi shi.
Tun a cikin Jam’iyyar sa, Trump ya buga da su; Ted Cruz, Ben Carson, Marco Rubio, Jeb Bush da su Gwamna Kasich, amma duk sun buga sun bar sa. Paul Ryan, wanda yake Shugaban Majalisar Kasar, ya nuna adawar sa a fili ga Trump, duk da suna Jam’iyya daya, hakan kuwa ya ma kara masa farin jinni. Kai har su John Mc Cain sun yi ta da Trump, amma wane mutum?

 
Trump: Kwangiri, karfen jirgi
Duk yadda za ayi a kauda Donald Trump an yi, amma Gogon ba ya jin bugu. Ga shi dai an fi sa kashe kudi wajen Yakin neman zaben, Shugaba Obama da kan sa, ya tashi tsaye wajen ganin Hillary ta kawo Amurka, amma INA.
Trump ya iya magana, kamar yadda Sir Elton John ya fada, yana da shegen baki. Ko da yake cewa wasu lokutan akwai kazanta a maganganun, amma magoya bayan sa mutanen Amurka, abin da suke son ji kenan. An zarge sa da laifin lalata da matan mutane, ba ya biyan ma’aikata balle haraji, amma duk ya tsallake wannan. Ya zagi kowa, ya kuma kwana lafiya, har ‘Yan Jam’iyyar sa, ba su sha ba. Trump yayi rikici da ‘Yan Jarida, mata, Jama’a da dama, dsr, kuma bai yi nadamar hakan ba, sam.

Zargin da ke kan Misis Clinton
Lokacin da Hillary Clinton ta ke Gwamnati ta goge Sakonnin Email sama da 30,000 daga akwatin ta na gida, Trump yayi amfani da wannan laifi ko abin da za a kira sa wajen doke Clinton. Trump har yayi ma Clinton alkawari zai daure ta saboda wannan idan ya hau mulki. James Comey na Hukumar Bincike na Amurka ya kara tado maganar daf da zabe da baki suka yi yawa.
Yayin da Clinton ke kokarin wanke kan ta, Trump ya shiga wanke tunanin magoya bayan ta. Hakan ya taimaka masa ainun wajen lashe ko samun kuri’u masu tsoka a inda Clinton ke da wayau. Trump ya ratsa Garuruwan da ake tunanin sun fi karfin sa a wannan lokaci, ko da ya gane yadda Sakamakon zaben da aka rika gudunarwa a Gidan Talabiji suke tafiya.



Trump ya fito a mutum
Donald Trump yayi wani irin yakin neman zaben da ba a taba yin irin sa ba a Tarihi. Trump ya caccaki wanda ya ga dama, yayi gatse, yayi zage-zage, yayi rikici da dan kowa, kai har magoyan bayan sa, sai suna hakuri da shi.
Trump bai yi ta mutane ba, ko yayi amfani da siyasa ko ya rika saka ma bakin sa linzami, A’a, namijin ba ruwan sa, wasu kuma hakan suke so, ko da basu fito fili ba. Yayin da wasu irin ‘Yan Boko ke masa kallon mahaukaci, yau ga wannan mahaukaci ya zama Shugaban Kasa na Amurka.

Muhammad Malumfashi ya fassara wannan daga BBC

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...