Thursday, November 17, 2016

Gwamnan Benue yayi kaca-kaca da Sarkin Musulmi




Sarkin Musulmi bai san yadda abin yake ba-Gwamna Ortom



Gwamnan Jihar Benue yace Sarkin Musulmi ya jahilci dalilin bude filin jirgin sama a Jihar



Kwanakin baya Sarkin Musulmi yace bai dace a bude filin jirgin sama ba



Sai dai Gwamnan na Benue yace duk wanda ya fadi haka jahili ne ko wanene

 

Gwamnatin Jihar Benue ta kare kan ta da yunkurin bude filin saukar jirgin sama a Jihar. Gwamna Ortom yake cewa duk wanda ya soki maganar bude filin jirgin sama a Jihar to jahili ne, bai fahimci lamarin Jihar ba ko kuma hassada ce kurum, kuma komai ilmin mutum.

Kwanakin baya kadan Sarki Musulmi, Abubakar Sa’ad yake cewa bai dace a rika gina filayen saukan jiragen sama ba, yayin da ake fama da hanyoyin titi a Kasa marasa kyau. Gina filin jirgin sama dai yana da matukar tsada, bayan jama’a da dama ma mutuwa a hanyoyin Kasa.

Shi dai Gwamna Ortom bai ji dadin wannan magana ba, yace Sarkin Musulmi bai fahimci lamarin bay a tsoma baki.

Mafi yawan mutane dai ba su cika hawa jiragen sama ba a Yankin, ko ka ga akwai filin saukar jirgi a makwabta. An fi hawa motoci, sau dama sai ka ga an kashe kudi alhali ba a amfani da filyane jirgin. Yayin da tituna ke bukatar gyara

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...