Zaben Donald Trump: Musulmai suna ta Lahaula
– Musulman duniya sun rikice bayan da Donald Trump ya samu nasara a zaben Kasar Amurka
– Musulmai na tsoron za ayi ta kashe su a duniya
– Donald Trump yayi alkawarin hana Musulmai shiga Kasar Amurka
Syed Chowdhury, wani Musulmi
dan Kasar Bangladesh yace Amurkawa sun ja wa duniya bala’i, watau da suka zabi
Donald Trump Shugaba. Musulmai fiye da Biliyan daya a duniya suna tunanin yadda
abubuwan za su kasance bayan da Donald Trump ya lashe zaben Kasar Amurka.
Wata Baiwar Allah ta ke cewa
‘Ya ‘yan ta ka da su kara saka Hijabi daga yau, tun da Donald Trump yaci zabe.
Wani yake cewa bai san yadda ‘Yan Gidan su za su yi ba. Alijah Diete, wani dan
gwagwarmaya daga Indonesia yake cewa: ‘Ina
tsoron za a shiga Yaki, Amurka tayi ta kashe mutane na Kasashen Musulmai’
Wani Farfesa, Zuhairi
Misrawi yace babu wadanda za su fi kowa murnar nasarar Trump, sai ‘Yan ta’adda
na Kungiyar ISIL. Ishaq Khan yace ya so ace Hillary Clinton ce taci zabe, da
Pakistan ta zauna lafiya. Khan yace Donald Trump fada da Musulmai zai yi, ban
ji dadi da yaci ba. A Garin Dubai ma dai, duk mutanen na cikin wani yanayi na lahaula, bayan da
aka ce Trump yaci zabe.
A gida Najeriya kuma, Farfesa Wole Soyinka yace
Najeriya da sauran Kasashen Afrika musamman na Yamma ba za su rika samun irin
taimakon da suka rika samu a lokacin Shugaba Barrack Obama ba. Minista Audu Ogbeh yace Sabon Shugaban Kasa Donald Trump dan jari-hujja ne, zai
kuma kashe Kasar Amurka. Shi kuwa Ministan Tsaro na
Kasar, Birgediya-Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya, cewa yayi dole a rungumi
kaddara.
No comments:
Post a Comment